Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa duk da hukuncin da kotun koli ta yanke kan cin gashin kan kananan hukumomin, har yanzu da sauran rina a kaba.
Haka kuma babbar jam’iyyar adawar ta ce tana nazari kan martanin da suka biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke, tana mai cewa zai yi wuya a iya raba gwamnatin jiha da kananan hukumomi.
- An Yi Watsi Da Ayyuka Na Fiye Da Naira Tiriliyan 17 A Nijeriya – Cibiyar CIPMN
- Matsalar Tsaro Da Hadurran Kwalekwale Da Ambaliyar Ruwa Na Cin Rayuka A Arewa
Jam’iyyar ta bayyana matsayinta ne ta bakin sakataren yada labaranta na kasa, Honarabul Debo Ologunagba, yayin da yake jawabi ga manema labarai a shalkwatan jam’iyyar na kasa a ranar Lahadin da ta gabata.
Da yake amsa tambaya kan matsayin Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, kan hukuncin kotun koli, Ologunagba ya ce, “Mun yi imanin cewa idan har za a yi wa kananan hukumomi garambawul, ya kamata a yi shi tare da gwamnoni ta yadda za su dace da bukatun gwamnatin tarayya.
“Tabbas, na yi imanin hakan ba zai kawo karshen lamarin ba, kamar yadda muke Magana saboda mutanen da ke da alhakkin kananan hukumomi su ne gwamnoni.
“Gwamnatin tarayya ba ta ganin mutane a kauyuka, gwamnoni ne suke yin hakan. Don haka idan akwai damuwa, to a hada kai da kananan hukumomi domin amfanar da al’umma, ba wai bukatar wasu ba.
“Doka ba ta nuni da abin da ba zai yiwu ba. Idan ta yi nuna da wani abu, za ta fadi hanyar warware duk wata matsala. Na tabbar da cewa mu ba mu ga cewa za a kawo karshen lamarin ba dangane da gudanar da kananan hukumomi.
“Gwamnatin jiha tana da alhakkin kan kananan hukumomi. Idan an samu matsala a kananan hukumomi, ba za su kira gwamnatin tarayya ba, za su kira gwamnatin jiha ne.
“Don haka dole ne a fahimci cewa gwamnatin jihar tana da hakki kan gudanar da harkokin kananan hukumomi, kuma abin da zai iya aiki a kai shi ne hanya mafi dacewa da za a ba da damar gudanar da ayyukan gwamnatin jihar, tare da gwamnoni da tsarin mulki ya tanadi hadin gwiwar asusun kananan hukumomi.
“Kudin tsarin mulki ya tanadar da shi ba gwamnatin tarayya ba ce ta tanadar da shi ba. Don haka a wane lokaci ya zama mara amfani?
“Haka kuma, ana ci gaba da tattauna wadannan batutuwa. A matsayinmu na jam’iyya, za mu yi ta tattaunawa a kai. Za mu kara tattaunawa da gwamnoninmu domin samun mafita.
“Na yi imanin cewa a karshe gwamnonin suna da rawar da za su taka dangane da gudanar da harkokin kananan hukumomi, saboda su suke da hakki fiye da kowa. Ina nufin dukkan alhakin gudanarwa, ba na tunanin za a kawo karshen wannan dambarwa.”
Mai magana da yawun jam’iyyar PDP ya ce damuwar jam’iyyar a fili take, domin kuwa kananan hukumomi suna da alaka da jihohi saboda sun fi kusa da juna.
“Yanzu a matsayinmu na jam’iyya, muna duba wannan hukuncin kotun koli a matsayin wani abun damuwa. Kuma zan fadi haka ne kasancewar gwamnatin tarayya na kokarin sake kirkiro wani tsarin mulkin kama-karya ko karkatar da al’amuran kananan hukumomi, muna ganin hakan zai zama wata hanyar kawo babbar matsala.”