Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da sabbin ka’idoji na sarrafa hada-hadar kasuwancin ‘PoS’ a fadin kasar nan, inda ya ba da umarnin cewa duk wani ciniki na POS zai bi ta ta hanyar cibiyar hadakar hada-hadar bankuna wato NIBSS ko UPSL, wanda wannan zai karya ikon tsohon tsarin da ake a kai na sarrafa mu’amalar kudi.
A cikin wata sanarwa mai kwanan ranar 11 ga watan Satumba, 2024 zuwa ga duk masu ba da sabis na hada hadar kudi zuwa kan PTSA (Payment Terminal Serbice Aggregators), CBN ta umurce su da su fara daidaitawa tare da PTSAs sannan su kuma sanar da CBN a rubuce domin tabbatar da bin wannan doka a cikin kwanaki 30 daga kan kwanan watan wannan takarda.
- Anya Barcelona Za Ta Iya Kai Bantenta Kuwa A Gasar Zakarun Turai Ta Bana?
- Nijeriya Za Ta Ci Gajiyar Dala Tiriliyan 7 A Tsarin Kasuwancin Musulunci Na Duniya
Domin cimma manufar bin diddigin hada-hadar kasuwancin kudade a Nijeriya, CBN a watan Agustan 2011, ya ba da lasisin PTSA ga NIBSS.
Biyo bayan damuwa game da bayar da damar lura da duk wani sha’anin kudi ta PoS ga cibiya guda ɗaya tal, a ranar 19 ga Afrilu, 2024, ta ba da lasisin PTSA na biyu zuwa ga UPSL (Unified Payment Serbices Limited).Kusan watanni biyar bayan da ta ba da lasisi ga UPSL, CBN ya ba da umarnin cewa masu wannan hulda su “sanya duk wata mu’amalar kudi dake gudana a PoS a wuraren kasuwanci imma a zahiri, ko a kan manhajar PoS na zahiri ko na badini, ta hanyar PSTA da suke da lasisi da CBN.”Sanarwar ta ci gaba da cewa, “ana bukatar PTSAs su aika da mu’amalar PoS zuwa ga kawai ma’aikatan da aka sahhalewar lura da tsarin hada hadar kudi, wanda masu sha’anin kudi suka ayyana kuma CBN ta ba su lasisi. Dole ne dukkan masu sarrafawa wadanda suke da lasisi a hada su da PTSAs, ta yadda za a bai wa masu hulda damar zabar wacce hanya da kuma PTSA za su yi amfani da su.“Duk cibiyar da ke lura da sha’anin kudi (PTSPs) dole ne su tabbatar da cewa an saita na’urorin PoS, manhajarsu da ayyukansu da kuma mu’amalar kudada ta hanyar PTSA, kamar yadda aka bada umurni. Duk PTSPs za su gabatar da bayani a kowanne wata ga CBN, suna mai bayyana adadin ‘yan kasuwa da wakilan da suke gudanar da aiki a karkashin su, tare da ayyukan PTSA da ake amfani da su wajen tafiyar da hada-hadar da ta dace.“Kowacce PTSA ana bukatar ya gabatar da kudaden da aka samu a kowanne wata ga CBN, tare da bayar da cikakkun bayanai game da duk wata hada-hadar da aka sarrafa ta hanyoyin sadarwar su. Ana sa ran gabatar da wannan bayani da aka ambata a sama ga Daraktan lura da sashen kula da tsarin biyan Kudi, kasa da kwanaki bakwai bayan karshen kowanne wata.