Kadarorin fansho a kasar nan, sun karu zuwa Naira biliyan 345, wanda hakan ya nuna cewa, a watan Agustan 2024, sun kai jimlar Naira tiriliyan 21.
Har ila yau, kudaden adashin gata na kadarorin fanshon, a karshen watan Agustan 2024, sun kai Naira tiriliyan 21.14, sabanin Naira tirilyan 20.79, da aka samu a watan Yulin 2024, wanda hakan ya nuna cewa, sun karu zuwa Naira biliyan 345.65.
- MOFA: Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
- Ɗaliban Kwalejin Kimiyya Ta Jega Sun Yi Zanga-Zanga Har Da Ƙone-Ƙone
Bisa bayanan da aka samu na baya- bayan nan, daga hukumar fansho ta kasa (PenCom), yawan ma’aikatan da suka yi ritaya suka kuma zuba kudadensu na yin ritaya a cikin asusun ajiya na masu ritaya wato (RSA), sun karu zuwa 10, 457,073 a karshen watan Augustan 2024, daga 10,419,520 da aka samu a watan Yuli.
Gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da kasancewa, a kan gaba wajen cin bashi daga asusun ajiya na ‘yan fansho da suka yi ritaya a matsayin ma’aikatan gwamnati.
Adadin kudin da gwamnatin ke zubawa, sun kai yawan Naira tiriliyan 13.40, a watan Agusta, wanda kuma kudin da gwamnatin ta zuba suka kai yawan Naira tirilyan 12.59, inda kuma sauran Naira tirilyan 2,04, ke bi a baya, sai kuma shiya din cikin gida da suka kai Naira tirilayan 1.94.
Bugu da kari, bisa bayanan da aka samu daga PenCom, a zango na biyu na 2024, jimlar dai-daikun mutane da wadanda suka zuba kudadensu a cikin asusun RSA sun kai Naira biliyan 377, wanda kuma daga bangaren na gwamnati, aka zuba Naira bilyan 217, sai kuma a bangaren masu zaman kansu, suka zuba Naira bilyan 160.83.
Hakan ya nuna yadda aka kawo karshen shekara, aka samu gibi a tsakanin wadannan bangarorin biyu, da ke nuna yawan abun da suka yi saura.
A zango na biyu na 2020, bangaren gwamnati ta zuba Naira biliyan 118.50, inda kuma na masu zaman kansu, aka zuba kasa da Naira biliyan 70.69.