Jam’iyyar NNPP ta zargi jam’iyyar APC mai mulki da kitsa rikicin da ya barke a wasu jam’iyyun adawa a kasar domin ci gaba da rike madafun a 2027.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban jam’iyyar na kasa, Ajuji Ahmed, ya bayyana shirye-shiryen hada kai da wasu sauran jam’iyyun siyasar kasar nan domin kawar da jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2027 mai zuwa.
- Sin Ba Za Ta Canza Matsayarta Game Da Mayar Da Hankali Kan Kasashe Masu Tasowa Ba
- Kashi 4.1 Na ‘Yan Nijeriya Ne Kawai Za Su Amfana Da Tsarin Mafi Karancin Albashi —Bankin Duniya
Ajuji wanda ya bayyana hakan a lokacin yakin neman zaben dan takarar gwamnan Jihar Ondo na jam’iyyar, Olugbenga Edema, ya yi zargin cewa jam’iyyar APC na tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu jam’iyyu domin raunana tsarin jam’iyyun da kuma kwace iko.
A cewarsa, jam’iyyar APC ta kammala shirye-shiryen wargaza maganar da ‘yan adawa suka yi domin hada karfi da karfe wajen yakar APC a zabe mai zuwa.
“Jam’iyyar APC tana yin duk mai yiwuwa domin ganin ta lashe zaben 2027. Tabbas, a ko’ina akwai shaida cewa suna tsoma baki a cikin harkokin jam’iyyun adawa.
“Amma ya rage ga sauran jam’iyyar siyasa su kiyaye mutuncinsu tare da tabbatar da cewa sun ci gaba da zama ‘yan adawan APC kafin da kuma bayan zaben 2027,” in ji Ajuji.
Ya yi kira ga jam’iyyar APC mai mulki da ta shirya mika mulki ga jam’iyyar adawa bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta hada kai da jam’iyyun adawa domin samun nasara a zaben 2027.