Ministar jin kai da walwalar al’umma, Sadiya Farouk, a ranar Talata ta kaddamar da rabon tallafin kudi ga mata sama da 3,500 a jihar Gombe.
Ministar ta bada tallafin ne karkashin shirin taimakon mutane da suke fama da matsanancin talauci da ake wa lakabi ‘Conditional Cash Transfer’ (CCT) a turance.
- NBC Ta Ci Tarar Trust TV Tarar Miliyan 5 Kan Yada Ayyukan ‘Yan BindigaÂ
- An Harbe Dogarin Mataimakin Sufeton ‘Yansanda Yayin Wani Harin ‘Yan Bindiga A Kaduna
Da take jawabi a yayin kaddamar da rabon kudin tallafin a babban zauren taro na gidan gwamnatin Gombe, ministar ta bayyana cewa wadanda aka zaba don cin gajiyar tallafin za su karbi Naira 20,000 kowannensu.
A cewarta, shirin tallafin na CCT na daya daga cikin abubuwan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kirkiro karkashin tsarin rage talauci da inganta walwalar al’ummar kasa, wanda yake mika taimako ga mutanen da suka fi fama da talauci musamman a yankunan karkara.
Ta yi ikirarin cewa gwamnatin Buhari ta gaji talauci wajen kaso saba’in daga gwamnatocin baya, shi yasa ta mayar da hankali wajen samar da hanyoyin rage wahalhalun jama’a.
“Wannan shirin yana daga wadanda suka fi ko wanne tasiri a nahiyar Afrika wajen rage fatara a tsakanin al’umma da kuma janyo hadaka daga kasashen duniya don inganta rayuwar al’umma”. Inji ministar.
Sadiya ta kara da cewa ita da kanta ta ga mutanen da a baya suke cikin mawuyacin hali amma yanzu sun canza sakamakon wannan tallafin da aka basu a sassa daban-daban na kasar nan.
Shi ma da yake jawabi, gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya wanda mataimakin gwamnan, Manasseh Jatau, ya wakilce shi ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa tallafin yana mai cewa tallafin zai kara wa wadanda suka ci gajiyarsa hanyoyin samun kudin shiga.
Ya kuma shawarci wadanda suka karbi tallafin da su yi amfani da kudin a kasuwanci da sana’oi da za su janyo musu riba.