Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke, wanda aka fi sani da “Gwamnan Mai Rawa”, ya samu lambar yabo ta LEADERSHIP ta Gwarzon Gwamnan Shekara saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen kawo sauyi da yawa a Jihar Osun.
Jagorancinsa ya ƙunshi inganta ababen more rayuwa da samar da walwalar ma’aikata da tsofaffi da bunƙasa harkokin noma da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa. Wannan karramawa ta nuna yadda jagorancinsa ke inganta rayuwar al’umma cikin gaskiya da aminci.
- Gwarzon Ɗan Siyasar Shekarar 2024: Adams Oshiomhole (CON)
- Gwarzon Gwamnan Shekara Ta 2024: Alhaji Abba Kabir Yusuf
Tarihi da Karatunsa;
An haifi Adeleke a Jihar Osun. Ya fara karatunskaratu a firamare ta Methodist da Nawarudeen, ya yi makarantar sakandare ta Ede Muslim Grammar School Ede, daga nan kuma ya ci gaba da karatunsa a Jami’ar Atlanta Metropolitan State College, inda ya samu digiri a ɓangaren shari’a kan manyan laifuka (Criminal Justice) a 2021. Daga ya ci gaba da ƙara zurfafa iliminsa.
Sanata Adeleke ya fara siyasarsa a 2017, lokacin da ya tsaya takarar Sanatan Osun ta Yamma bayan rasuwar ɗan uwansa, Sanata Isiaka Adetunji Adeleke. Duk da cewa a lokacin yana sabuwar fuska a harkar siyasa amma ya samu nasarar lashe kujerar, duk da kasancewar APC ce mai mulki a jihar.
A 2018, ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, inda ya sha gwagwarmayar shari’a kan takararsa. Duk da rasa nasara a kotun ƙoli, ya sake jajircewa da shiryawa don takarar gwamna a 2022, inda ya samu nasarar doke gwamna mai ci, Adegboyega Oyetola. Wannan ya tabbatar da karɓuwarsa a tsakanin jama’ar jihar.
Nasarori A Matsayin Gwamna;
Bayan hawa mulki, Adeleke ya mayar da hankali kan cika alƙawurran da ya ɗaukarwa al’ummarsa yayin yaƙin neman zaɓe. Ya fara kammala ayyukan da aka bari ba a ƙarasa ba, tare da ƙaddamar da sababbin ayyukan da suka shafi rayuwar jama’ar jihar kai-tsaye, kamar hanyoyi da gadaje da gina titunan a faɗin jihar. A cikin watanni 11 na farkon mulkinsa, Adeleke ya fara gadoji a Osogbo da Ile-Ife da Ilesa da kuma Ede. Ya ƙaddamar da tsarin Naira biliyan 100 don ci gabagaba da gudanar da manyan ayyuka ba tare da dogaro da cin bashi ba.
Gwamna Adeleke ya tabbatar da biyan albashi da fansho akan lokaci, yana cika alƙawarinsa na biyan albashin da aka bari bashi a baya. Wannan ya ja hankalin ma’aikatan Jihar Osun, inda suke masa laƙabi da “Mutum na mutane”.
Noma da Kiwo;
Adeleke ya mayar da hankali kan bunƙasa harkokin noma domin inganta samar da abinci da tattalin arziƙin jihar. Ya raba injinan noma da kayan aikin gona ga manoma, ya kuma ƙaddamar da tsarin Osun Broilers Outgrower, wanda ya bayar da tallafi ga masu kiwon Kaji.
A ɓangaren ilimi kuwa, Adeleke ya dawo da tallafin karatu ga ɗalibai a manyan makarantun jihar, ya kuma tabbatar da fara aikin Jami’ar Ilesa da kuma gyaran makarantu a faɗin jihar. Wannan ya ƙara wa yara damar samun ingantaccen ilimi a tsari mai kyau da tsaro.
A ɓangaren lafiya, ya gyara tare da gina sababbin cibiyoyin lafiya sama da 120 daga cikin 345 da ake shirin sabuntawa a jihar. Kazalika, ya gabatar da shirye-shiryen lafiya kyauta, ciki har da tiyatar ido, wanda ake gudanarwa a duk faɗin jihar don tallafa wa jama’a.
Tallafi ga Mata da Matasa
A ƙarƙashin shirin Opon Imo Empowerment, Gwamna Adeleke ya samar da tallafi da horo ga matasa da mata don kafa ƙananan sana’o’i. Wannan ya rage zaman kashe wando tare da ba su damar samun dogaro da kai.
Adeleke ya shahara da halin kula jama’arsa, inda yake sauraron ƙorafe-ƙorafensu tare da mayar da hankali kan ayyukan da za su amfani al’umma. Wannan salon jagoranci ya ƙara masa farin jini da karɓuwa a zuƙatan jama’a, inda ake ganinsa a matsayin jagoran da ke kula da al’ummarsa. Jagorancin Adeleke ya kawo sauyi a Jihar Osun, inda ya tabbatar da cewa kowanne ɓangare na rayuwar al’umarsa sun samu ci gaba.