Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta guji tsoma baki a al’amuran da suka shafi hurumin gwamnatin Kano.
Wannan kalaman sun biyo bayan gargadin ta’addanci da Rundunar ‘Yansandan Kano ta fitar, wanda Kwankwaso ya bayyana a matsayin marar muhimmanci kuma mai cutarwa ga muradun jihar.
- Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya
- Nan Ba Da Jimawa Ba Za Mu Fara Zawarcin Kwankwaso – PDP
A ranar Litinin, Kwankwaso ya taya ƙungiyar Tijjaniyya murnar gudanar da Mauludin Shehu Ibrahim Inyass a Sani Abacha Stadium, Kano. Ya yabawa Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, da Gwamnan Kano, Abba Yusuf, kan shirya taron. Sai dai ya nuna damuwa kan gargadin da Ƴansanda suka fitar kafin taron, yana mai cewa hakan ya haifar da tsoro ga mazauna jihar da baƙi.
Kwankwaso ya soki gargadin a matsayin mara tushe, yana mai cewa hakan ya raunana ƙwarin gwuiwar jama’a ga Ƴansanda. Ya kuma bayyana cewa irin wannan matakin zai iya haifar da sakaci idan barazana ta gaske ta taso a gaba.
“Fitar da irin wannan gargadin da bai tabbata ba yana kawo tarnaki ga martabar rundunar ‘yan sanda, musamman a idon duniya,”
in ji shi.
Sanatan ya yi kira ga Ƴansanda da su kasance masu kwarewa a aikinsu, tare da nisantar duk wani abu da zai nuna su a matsayin masu son ɓangaranci. Har ila yau, ya jaddada buƙatar Gwamnatin tarayya ta mutunta ikon Kano da guje wa tsoma baki a al’amuran jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp