Aiwatar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi ya fuskanci matsaloli da dama watanni bakwai bayan hukuncin kotun koli.
Lauyoyi sun bayyana damuwarsu kan yadda aka jinkinta aiwatar da hukuncin kotun koli, wanda suka nuna cewa ba a mutunta hukuncin kotun kolin tare da nuna yadda gwamnatin Nijeriya ke yawan kauce wa hukuncin shari’a.
- An Bude Cibiyar Tattarawa Da Yada Labarai Ta Taruka Biyu Na Sin
- Gwamnatin Kano Za Ta Ɗau Nauyin Ɗalibai 1,002 Domin Karatu A Ƙasashen Waje
A ranar 11 ga Yuli, 2024, kotun koli ta ba da umarnin cewa dole ne a biya su kason kananan hukumomi kasonsu kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya, kamar yadda babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, SAN, ya bukata a karar da ya shigar a gaban kotun koli.
Fagbemi dai ya shigar da karar ne a madadin gwamnatin tarayya, inda ya nemi a ba da cikakken ‘yancin cin gashin kai da samar da kudade kai tsaye ga daukacin kananan hukumomi 774 na kasar nan.
Ya bukaci kotun kolin da ta bayar da umarnin haramta wa gwamnonin jihohi ba tare da bin doka ba su rusa shugabannin kananan hukumomin da aka zaba.
Sai dai gwamnatocin jihohi 36, ta hannun lauyoyinsu, sun shigar da kara a gaban kotun, inda suka ce kotun koli ba ta da hurumin sauraren karar.
Sun kuma kulubalanci babban lauyan gwamnatin tarayya cewa bai da hurumin kai karar a madadin kananan hukumomin.
Duk da haka, kotun kolin ta tabbatar da huruminta. A wani hukunci da mai shari’a Emmanuel Agim ya karanta, kotun ta ce ci gaba da rike kudaden kananan hukumomi ya saba wa kundin tsarin mulkin asa.
Duk da haka, kotun kolin ta tabbatar da huruminta. A wani hukunci da mai shari’a Emmanuel Agim ya karanta, kotun ta ce ci gaba da rike kudaden kananan hukumomi ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan.
“Akwai bukatar yin adalci domin ci gaba da dorewar doka. Matsayin wannan kotun shi ne, gwamnatin tarayya ta iya biyan kudaden kananan hukumomi kai tsaye ba hannun jihohi ba.
“A wannan yanayin, tun da biyan kudi ta hanyar jihohi bai yi aiki ba, bisa adalcin wannan kotu, ta zartar da hukunci cewa a biya kananan hukumomi kasonsu daga asusun tarayya kai tsaye,” in ji kotun.
Kotun koli ta kara ba da umarnin hana wadanda ake tuhuma da wakilansu ko kuma ba su kariya daga kashe kudaden kananan hukumomi. Ta kuma bayyana cewa ka da wata gwamnatin jiha ta karbi kudaden kananan hukumomi.
Bugu da kari, kotun ta ce gwamnatocin jihohi ba su da ikon nada kwamitocin rikon kwarya kuma kananan hukumomin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya ne kadai doka ta amincewa da su.
Haka kuma, kotun kolin ta umurci gwamnatin tarayya da ta zartar da wannan hukuncin cikin gaggawa.
Sai dai, maimakon zartar hukuncin kotun koli cikin gaggawa, gwamnatin tarayya da na jihohi sun yi danwaken zagaye da hukuncin da kuma kokarin kaucewa aiwatar da shi.
Lauyoyin sun nuna damuwarsu kan yadda gwamnatin tarayya ke kin aiwatar da hukuncin kotun koli wajen zubar da mutuncin ikon bangaren shari’a.
Kotun koli ita ce ke da hurumin yanke hukunci na karshe, kuma hukuncin ya shafi dukkan kananan kotuna da wadanda abin ya shafa, kamar yadda sashe na 233 na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 ya tanada.
Rahotanni sun bayyana cewa yunkurin farko na kawo cikas ga aiwatar da ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi shi ne, na dakatarwar da gwamnatin tarayya ta yi wa gwamnoni na tsawon watanni uku a watan Agustan 2024.
Gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi sun amince da dakatarwar ne a kan matsalolin da ke tattare da tasirinsa wajen biyan albashi, yadda ake gudanar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp