Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa Ta ƙasa NPA da Kwalejin Horas da ɗirebobin Jiragen Ruwa ta ƙasa wato, MAN da ke a Oron, sun ƙaddamar wasu sauye-sauye na ƙara ƙarfafa bunƙasa ayyuka da kuma ƙara haɓaka, ayyuka da ake gudanarwa, a Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar nan, mussaman domin a Nijerya ta ƙara amfana da tattalin arzikn da ke a Teku.
Wannan bayanin, na ƙunshe ne, a cikin rahoton da mahukuntan NPA na shekarar 2024.
A cewar rahoton, an samu ƙarin zuba hannun jari daga kaso 45.1 ko kuma ƙarin kaso 71.2 na metric tan miliyan 103.3 zuwa tan miliyan daga shekarar 2023 zuwa shekarar 2024.
- Shekara 61 Da Haihuwar Sam Nda-Isaiah: Waiwayen Mukarrabai Kan Mashahuran Hikimominsa
- Manyan Nasarorin Da Dakta Dantsoho Ya Samar Tun Darewarsa Shugabancin NPA
Rahoton ya ƙara da cewa, wannan nasarar, taimaka wajen ƙara haɓaka ingancin ayyukan da ake gudanarwa, a Hukumar ta NPA
Kazalika, a cewar wasu alƙaluman da suka fito daga babban taron bunƙasa tattalin arziki wato NESG, rahoton ya nuna yadda aka samu ƙarin gudanar da hada- hadar cinikayyar ƙasar nan ta kai daga Naira tiriliyan 5.81 zuwa ta dala biliyan 3.7 a zango na uku na na shekarar 2024.
Bugu da ƙari, Hukumar ta NPA ta bayyana cewa, tana kan ƙoƙarin inganta kayan aiki Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar, wanda ta zuba dala biliyan daya, domin fara gyaran Tashoshin Jiragen Ruwa ta Tin Can Island tare da yin ayyukan kwakwarima, a Tashoshin Jiragen Ruwa na, Apapa, Riɓers, Onne, Warri da kuma Kalaba.
Ita kuwa a na ta ɓangaren, Kwalejin ta MAN ta bayyana cewa, nauyin da aka ɗora mata na gudanar da ayyukan ta, son yi daidai da ƙoƙarin ƙasar nan ke ci gaba da yi, na ƙara haɓaka tattalin arzikin ƙasar, mussaman wajen yaye haziƙai kuma ƙwararrun ɗirebobin Jiragen Ruwa da ƙasar nan ke buƙata.
Shugaban Hukumar ta NPA darka Abubakar dantsho, a jawabinsa ewabinsa a taron shekara- shekara na ƙasa na shekarar 2025 na ƙungiyar ƴanjarida da ke dauko rahotabin da suka shafi fannin ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa wato AMJON ta gudanar a dakin taro na otel ɗin Sheraton Hotel da ke a, Ikeja a jihar LegasLegas, ya bayyana cewa, Hukumar ta NPA, na kan gudanar da aikin fadada Sabbin Tashoshin Jiragen Ruwa na Snake Island, Badagry ɗeep Seaport, Ondo ɗeep Seaport da kuma ta, Burutu wadanda daukacin aikin, a yanzu suka kai matakin kammalawakammalawa
dantsho wanda Babbar Manajar huɗda da Juma’a a Hukumar ta NPA Hadiza Usman Shu’aibu ta wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa, Hukumar ta NPA, ta mayar da hankali wajen ganin tana ƙara daga nartabar kayan aikinta da ke a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwa na ƙasar,mussaman ta hanyar sanya masu kayan aiki na zamani, domin a rinƙa Kula da saukar Jiragen Ruwa da ƙara janyo masu zuba hannun jari, a fannin.
Shugaban ya ci gaba da cewa, a yanzu haka, Nijeriya ta samu samar shiga cikin ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta Kula da tsara Tashoshin Jiragen Ruwa wato IPCSA wanda ya samar da cewa, wannan shigar ta Nijeriya cikin ƙungiyar, zai bai wa Nijeriya damar wanzar da tsarin NSW wanda aka samar da shi, bisa nufin saita ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa da kuma rage ƙalubalen da ake fuskanta ta hada-hadar kasuwanci.
Kazalika, dantsho ya bayyana cewa, Hukumar ta NPA, ta samu nasarar rage ƙalubalen cunkodon ababen hawa da ake fuskanta a Tashoshin Jiragen Ruwan ƙasar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp