A ranar Litinin din makon jiya ne Alkalin-Alkalan Nijeriya, Justice Ibrahim Tanko Muhammad ya yi murabus na radin kashin kai bisa hujjojin rashin lafiya da ya bayar.
Shi dai Justice Tanko a watan Janairun shekarar 2019 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da shi a matsayin mukaddashin Alkalin Alkalan Nijeriya bayan dakatar da Alkalin Alkalan wancan lokaci, Walter Onnoghen kan zargin da aka masa na kin bayyana kadarorin da ya mallaka a rayuwarsa.
Wannan matakin na murabus din Tanko na zuwa bayan da wasu manyan Alkalan Nijeriya su 14 suka yi ta korafin rashin samun ababen more rayuka da yanayin aiki mai inganci a karkashin jagorancin Justice Tanko, kodayake daga baya ya fito ya musu bayani dalla-dallah na dalilan da suka sanya wasu abubuwan da suke bukata bai samuwa.
Bayanai sun nuna cewa Mai Shari’a Olukayode Ariwoola shi ne alkali mafi girman mukami bayan murabus din mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, wanda kuma tunin shugaban kasa ya rantsar da shi.
A kan wannan kokarin nasa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karrama shi da lambar karamci ta kasa ta GCON.
Buhari a lokacin da ke rantsar da sabon babban jojin Nijeriya, Justice Olukayode Ariwoola a matsayin wanda ya gaji Tanko Muhammad.
Shugaban kasa ya jawo hankalin sashin shari’a da su kara azama a fagen aiki domin kada ‘yan Nijeriya su yanke kauna da fata daga garesu.
Shugaban kasan ya jinjina wa Tanko bisa irin nasarorin da ya iya cimmawa, don haka ne ya karramashi da lambar yabo ta GCON don nuna godiya da irin kokarinsa ga Nijeriya.
“Na amshi wasika daga wajen Honorabul Justice Dakta I. Tanko Muhammad CFR, na murabus dinsa a matsayin Alkalin Alkalan Nijeriya kuma shugaban majalisar shari’a ta Nijeriya bisa dalilai na rashin lafiya. Kuma murabus dinsa ta fara aiki nan take ne.
“CJN Tanko an nada a kotun daukaka kara a 2006, aka kuma rantsar da shi a ranar 8 ga watan Janairun 2007, ya zama babban Alkalin Nijeriya a matsayin mai rikon kwarya a ranar 25 ga watan Janairun 2019.
“An kuma rantsar da shi ya zama Alkalin Alkalai a ranar Laraba 24 ga watan July na 2019.” A cewar shugaban kasar, bisa yadda yake a tsare, tsohon CJN din ya kamata ne ya yi ritaya a ranar 31 ga watan Disamban 2023, amma bisa rashin lafiya ya amince ya ajiye aikin nasa.
Shugaba Buhari ya ce, sashin shari’a a karkashin jagorancin Tanko Muhammad an samu cimma nasarori masu tarin yawa da suka hada da yanke hukunci masu tarin yawa da tsare-tsaren da kotun daukaka kara ta samar, da kuma kara samar da wasu kotuna da kundin tsarin mulki ya samar, gami da yin aiki tukuru wajen bada hukunci ba tare da nuna son kai ko nuna bangaranci ba.
A cewar shugaban, tarihi ba zai mance da irin gudunmawar da Justice Muhammad ya baiwa sashin shari’a a Nijeriya ba, kyautata demoradiyya da cigaban kasa. Ya ce, a kan hakan ne suka duba dacewar bashi lambar yabo ta GCON.
Kazalika, shugaban ya bada tabbacin gwamnatinsa na cigaba da sake mara wa sashin shari’a a matsayin mai cin kashin kanta domin wanzar da adalci a kowani lokaci.
A jawabinsa bayan shan rantsuwa, sabon Alkalin Alkalan, Justice Ariwoola ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa ba zai taba watsa musu kasa a ido ba, zai yi iya kokarinsa wajen kyautata aiki domin lamura su dawo yadda suke.
Mukaddashin Alkalin Alkalan ya ce, “Abun da muke tsammani daga wajen ‘yan Nijeriya kawai su kasance masu bin dokoki da kwansitushin din kasa.”
Ya kuma ce babu wata baraka a sashin shari’a don haka ne yake mai tabbatar da cewa aiki zai inganta kuma jin dadi da walwalar alkalai zai kara samun tagomashi a karkashin jagorancinsa.
A gefe guda, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi fatan alkairi wa Justice Tanko Muhammad, ya kuma jinjina masa biya gudunmawar da baya bayar wa Nijeriya.
Sai ya jawo hankalin sabon mukaddashin CJN da ya yi amfani da gogewarsa wajen tafiyar da ayyukansa bisa tsarin doka da bin kwansitushin na kasa domin daurewar lamura da tafiyar da komai bisa gaskiya da adalci.