Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda shi ne sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, bayan amincewar taron NEC na 14 da aka gudanar a ranar Alhamis. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke ƙoƙarin sake daidaita kanta domin tunkarar ƙalubalen ciki da na zaɓen 2027.
An haifi Yilwatda a ranar 8 ga watan Agusta, 1968 a Dungung, ƙaramar hukumar Kanke ta jihar Filato. Ya yi karatu a Boys’ Secondary School Gindiri, sannan ya samu digiri na farko daga Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Makurdi, sai digiri na biyu daga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, da kuma digirin digirgir daga Jami’ar Nijeriya Nsukka a fannin Injiniyan Kwamfuta da Na’ura.
- Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa
- Mutumin El-Rufai, Baloni, Ya Fice Daga APC A Kaduna
Yilwatda ya yi aiki na fiye da shekaru 26 a Jami’ar Makurdi inda ya kai matsayin Darakta na farko a sashin ICT na jami’ar, inda ya jagoranci sauye-sauyen fasaha masu zamani. Ya kuma yi aiki da hukumomin ƙasa da ƙasa kamar EU, da UNICEF, da World Bank da TECHVILE USA, yana ba da shawarwari a fannin cigaban fasaha da shugabanci.
A 2017, an naɗa shi a matsayin kwamishinan zaɓe a hukumar INEC, inda ya jagoranci sauye-sauyen tsarin kaɗa ƙuri’a musamman ga ‘yan gudun hijira da masu buƙata ta musamman. Daga bisani ya sauka daga kujerar domin shiga siyasa, inda ya tsaya takarar gwamnan Filato ƙarƙashin APC a 2023, kuma ya jagoranci kamfen na Tinubu/Shettima a jihar.
Tun kafin naɗinsa a matsayin shugaban jam’iyya, Yilwatda yana rike da muƙamin Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, da kuma mamba a kwamitin tattalin arziƙin shugaban ƙasa. Kwarewarsa a fannin fasaha da shugabanci na ƙara tabbatar da cewa yana da cancanta a matsayin sabon jagoran jam’iyyar APC.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp