Ciwon Siga wata cuta ce dake da matukar hadari wadda ake kamuwa da ita lokacin da Pancrease wanda wani wuri a kusa da ciki wanda yake samar da sinadarin ‘INSULIN’ da kuma ruwan da yake taimakawa jiki narkar da abinci, ya kasance bai iya samar da sinadarin insulin,ko kuma lokacin da jiki ba zai iya yin amfani da shi.
Har yanzu ita ce cuta da take bada babbar matsala a karni na ashirin da daya, hakan ya kasance ne saboda matsalolin cututtukan da ake kamuwa da su.
- 2023: Gwamnatinmu Za Ta Farfaɗo Da Harkar ilimi Da Walwalar Malamai – Atiku
- LP, Ta Kori Daraktan Yakin Neman Zaben Obi, Okupe Da Wasu 11 Kan Gaza Biyan Harajin Jam’iyyar
Shugabar kwamitin amintattu ta wayar da kan al’umma wajen kokarin da ake yi na yakar cutar Dokta Afoke Isiabwe ta bayyana cewa cutar Siga ta shafi mutane kusan milyan 537 da kuma yara fiye da milyan 1.1 a fadin duniya wannan ya hada da ‘yan Nijeriya milyan ko wacce shekara.
Duk shekara cutar Siga tana kashe mutane kusan milyan hudu a duniya, ta dai kara jaddada cewa cutar tana iya shafar gaba daya ko wanne sashe na jiki.
Tana sanadiyar rashin gani na idanu, ga matsala mai shafar hakora, tsayawar aikin koda, cardiobascular disease, yanke hannu ko kafa, haduwa da matsala lokacin saduwa da mace, wannan sai idan ba a dauki matakan da suka dace ba.
Tace yawancin abubuwan da cutar siga ta 2 ana iya maganinsu ta hanyar tafiyar da rayuwa yadda ta dace.
Ta bayyana alamun jan kunne na kamuwa da cutar siga da suka hada da lokacin da mutum yake fama jin kishirwa ko shan ruwa,har abin ya wuce kima, ga kuma yawan fitsari, jiki ya kasance babu nauyi saurin jin gajiya ko ba wata laka.
Mutum ya kasance cikin damuwa ko ya kasance a wani sauyin yanayi, ba zai iya gani sosai ba, idan ya yi rauni ba zai bai warkewa, yasai kuma ta bayyana har ila yau alamu na an kamu, lokacin da mutum yake jin ya kamu da cuta, kamar cutar dasashi, fata da cututtukan Farji da dai sauransu.
Bugu da kari tace yakamata ‘yan Nijeriya da akwai sauran hanyoyin da ake kamuwa da cutar kamar tarihin iyali dangane da cutar siga, yin kiba ko nauyin da ya wuce misali,cin abincin da bai dace ba, rashin motsa jiki, karuwar shekaru, hawan jini, amfani da abincin da bai kamata lokacin da mace take da juna biyu.
Har ila yau da akwai:glucose da tarihin ciwon sukari na ciki suna da alaka da nau’in ciwon sukari na 2, nau’in ciwon siga na 2 wanda shi ne wanda aka fi sani, uwa uba kuma ga tarihin cutar sigar mata masu juna biyu kan kamu da ita.
“Da akwai bukatar kowa ya lura da su wadannan alamun na cutar siga, domin a samu daukar matakain daya kamata saboda san yadda za a kula da cutar da hanyoyin kauce ma kamuwa da ita,bare ma har ma ta kai ga yin kamari.
“Hakanan ma mutane da sduka riga siuka kamu da cutar siga suna da bukatar taimako daga ‘yan’uwansu domin su iya tafiyarda yawan kudaden da ake kashewa wajen kokarin rabuwa da ita, sai kuma irin kallon da za a rika yi masu da su kuma yadda za su ji a jikinsu sanadiyar kamwa da cutar sikari.
Akwai bukatar a rika cin abincin da ya dace musamman ma mai gina jiki, da ci gaba da yawan motsa jiki, ga kuma lura da kada a bari nauyin jiki yayi yawan daya wuce misali.Ana iya duk tafiyar da duk matakan matukar ko wadanne iyalai za su lura da kuma yin amfani da matakan.”
Ta yi kira da ‘yan Nijeriya su san abubbuwan da suka kamata su sani danagane da cutar siga, da hanyoyin kauce ma kamuwa da ita, da mace- macen da ake yi snadiyar cutar.
Wayar da kan al’umma shi ne babban mataki saboda mutanen da suke fama da cutar, da kuma wadanda aka gwada sun kamu da ita amma basu san hanyar da za su bi ba wajen neman maganinta.
Daga karshe Isiabwe tayi kira da gwamnatoci sai masu kula da lafiyar al’umma da masu ruwa da tsaki, su kara zage damtse wajen samar da hanyoyin wayar da kan al’umma yadda za su fahimci al’amarin, hakan zai taimaka masu wajen lura da alamun kamuwa da cutar, da matakan da suka dace na rabuwa ko warkewa daga cutar siga.