A yau Laraba, hukumar kula da hakkokin mallakar sabbin kirkire-kirkire ta kasar Sin (CNIPA) ta bayyana cewa, ya zuwa karshen watan Yuni, adadin hakkokin mallakar manyan sabbin kirkire-kirkire na kasar ya kai miliyan 2.36, lamarin da ke nuna karuwar ci gaban da ake samu a fannin samar da ingantattun kirkire-kirkire masu alaka da hakkin mallakar fasaha a kasar.
Har ila yau, kasar Sin ta samu ci gaba mai karfi wajen kirkire-kirkire a muhimman fannoni. Ya zuwa karshen watan Yuni, hakkokin mallakar kirkire-kirkire masu inganci a fannin fasahar bayanai ta zamanin gaba ciki har da kirkirarriyar basira ta AI, da sadarwar Intanet, da fasahar adana ayyukan kwamfuta a giragizan intanet, da kuma sarrafa manyan bayanai, sun kai kashi 16.5 na jimillar hakkokin mallakar kirkire-kirkire da aka bayar a kasar.
Ana sa ran cewa karuwar wadannan hakkokin mallaka cikin sauri a wadannan fannoni masu tasowa, za ta taimaka wajen tallafa wa sabbin ginshikan bunkasa tattalin arziki. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)














