A yau Talata, wata majiya daga maaikatar harkokin wajen kasar Sin, ta ce bisa gayyata da aka mika musu, wasu shugabannin kasashen waje za su halarci bikin bude baje kolin kasa da kasa, na hajojin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 9 a birnin Shanghai na kasar Sin. Za a gudanar da baje kolin ne tsakanin ranakun 5 zuwa 10 ga watan nan na Nuwamba, tare da sauran ayyuka masu nasaba da shi.
Majiyar ta ce shugabannin da aka gayyata sun hada da shugaban kasar Gabon Brice Clotaire Oligui Nguema, da shugaban gwamnatin Austria Christian Stocker, da mataimakin shugaban kasar Liberia Jeremiah Koung.
Sauran su ne mataimakin firaministan Cuba kana ministan harkokin kasuwancin ketare da zuba jari na kasar Oscar Perez-Oliva Fraga, da mataimakiyar firaminista kana ministan raya tattalin arzikin Slovakia Denisa Sakova. Sai kuma mataimakiyar firaminista, kana ministar raya tattalin arziki da ci gaba mai dorewa ta kasar Georgia Mariam Kvrivishvili. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














