Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe, ya bayyana cewa hukumar na nazarin yiwuwar komawa tsarin gudanar da gasar cin Kofin Ƙasashen Afirka (AFCON) duk bayan shekaru biyu, maimakon duk bayan shekaru huɗu. Motsepe ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a Cape Verde ranar Juma’a, yayin taron shekara-shekara na hukumar.
Wannan batu ya taso ne ƙasa da shekara guda bayan da CAF ta sanar a watan Disambar 2025 cewa za a riƙa gudanar da gasar AFCON duk bayan shekaru huɗu daga shekarar 2028. Hukumar ta kuma tabbatar da cewa Kenya, Tanzania da Uganda ne za su karɓi baƙuncin gasar ta shekarar 2027.
Sanarwar sauya tsarin gasar ta jawo ce-ce-ku-ce daga wasu masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafa, inda aka nuna damuwa kan dalilan da suka sa aka yanke shawarar. Wasu kuma sun yi zargin cewa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ce ta matsa wa CAF lamba domin sauya tsarin gasar, duk da cewa ba a tabbatar da wannan zargi ba.
Sai dai Motsepe ya jaddada cewa har yanzu ba a yanke wata shawara ta ƙarshe kan batun ba. Ya ce ana sa ran gabatar da shawarar gaban Kwamitin Zartarwa na CAF nan ba da jimawa ba domin tattaunawa da kuma yanke matsaya.
Taron na tsawon kwanaki uku ya haɗa shugabannin hukumomin ƙwallon ƙafa na ƙasashe 54 mambobin CAF, mambobin Kwamitin Zartarwa, masu horar da tawagogin ƙasashe da sauran masu ruwa da tsaki. Mahalarta taron sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi makomar ƙwallon ƙafa a Afirka da tsare-tsaren ci gabanta har zuwa shekarar 2030.














