Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ajandar ci gaban da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa ta ƙunshi dukkan sassan ƙasar ba tare da nuna ɓangaranci ba, inda ake gudanar da manyan ayyuka da shirye-shirye a faɗin ƙasa.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana haka ne a Abuja ranar Laraba, lokacin da ya karɓi baƙuncin Kwamishinonin Yaɗa Labarai na jihohi 36.
- Kowa Ya Ci Zomo Ya Ci Gudu: Shekaru 80 Da Nasarar Sinawa A Kan Zalunci Da Danniyar Japanawa
- Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Haifar Da Da Mai Ido A Katsina
“Ya ce: “Ban taɓa ganin inda ake da ayyukan yi amma Shugaban Ƙasa ya ƙi aiwatarwa saboda gwamnan wannan jiha ba ya cikin APC ba. A duk abin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, hankalinsa yana kan ɗan Nijeriya ne.”
Dangane da cire tallafin man fetur kuwa, ya ce hakan ya bai wa jihohi damar samun kuɗaɗe fiye da da domin aiwatar da ayyuka masu muhimmanci.
Ya ce: “Cire tallafin man fetur ya buɗe hanya da ta bai wa dukkan shugabanninku damar aiwatar da ayyuka da kawo wa jama’a amfanin dimokuraɗiyya. Ban ji wani gwamna ba, ko daga jam’iyyarmu ko wata jam’iyya, da ya ce mu dawo da tsohon tsarin.”
Idris ya tunatar da cewa kafin Tinubu ya hau mulki, jihohi 27 na fama da biyan albashi, sannan kashi 97 na kuɗaɗen shiga na ƙasa na tafiya wajen biyan bashi. Amma yanzu, a cewarsa, an samu sauyi saboda gyare-gyaren da Shugaban Ƙasa ya aiwatar.
Ya ce: “Nijeriya na kan tafiya zuwa ga ci gaba na dindindin da zai amfani kowa. Saƙona, da kuma saƙon da muke da shi a gare ku duka shi ne ku zo ku shiga wannan jirgi domin kai Nijeriya ga inda Shugaban Ƙasa ya yi alƙawarin kai ta, kuma wanda kuke so ku gani a ƙarshe.”
Haka kuma, Ministan ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta kai ziyara wasu jihohin Kudu maso Kudu da Arewa maso Gabas domin duba manyan ayyuka tare da tattaunawa da jama’a a matsayin wani ɓangare na tsarin samun ra’ayin jama’a.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Kwamishinonin Yaɗa Labarai, wanda kuma shi ne Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Borno, Farfesa Usman Tar, ya ce za su yi aiki tare ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa ba, domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da inganta ƙimomin al’umma.
Ya ce: “A gabanka akwai kwamishinoni daga jam’iyyun siyasa daban-daban, daga yankuna daban-daban na ƙasar nan. Saboda haka muna wakiltar sassa daban-daban na tarayyar Nijeriya. Ba mu zo a madadin wata jam’iyya ko wani muradi na kashin kai ba. Mun zo ne bisa wani dandali na ƙasa domin tattauna hanyoyi da dabarun inganta muradinmu na ƙasa, ɗabi’unmu da kuma wayar da kanmu”
Ya ƙara da cewa ƙungiyar tasu za ta ci gaba da goyon bayan ma’aikatar wajen yaɗa muhimman kamfen na ƙasa, ciki har da wayar da kai da tarukan tattaunawa da jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp