Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta jaddada mahimmancin hadaka da dagaro a tsakanin kasasehn da ke Afirka, domin a kara karfafa ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a daukacin nahiyar
Shugaban Hukumar Dakta Abubakar Dantsoho, ya bayyana haka a cikin sanawar da ya fitar a ranar Lahadi, yayin rufe taron karo na 45 na shekara-shekara na Kungiyar Masu Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Afirka ta Yamma wato PMAWCA da aka kammla a yankin Pointe-Noire na Jamhuriyar Kongo.
- Gwamnan Kano Ya Ɗauki Malaman Lissafi 400 Aiki
- Sace ‘Yan Makarantar Mata Ta Kebbi: Abubuwan Da Ba A Fada Ba
Dantsoho wanda kuma shi ne, Shugaban kungiyar, ya nuna matukar jin dadinsa kan yadda aka gudanar da tattaunawa a taron da kuma sakwanin fatan alheri da aka gabatar a taron wanda ya sanar da cewa, hakan ya nuna cewa, kasashen da ke ba cikin kungiyar, a shirye suke, domin ganin an kawo karshen kalubalen da fannin ke fuskanta.
Shugaban wanda Janar Manaja na sashen hulda da Jama’a a Hukumar Ikechukwu Onyemekara ya wakilce shi a wajen rufe taron, inda ya sanar da cewa, matsayar da aka cimma a wajen taron, za a yi amfani da su, wajen samar da tsare-tsare da karfafa yuinkurin matakan gwamnati da ke a cikin kasashen da ke a yankin na Afirka ta Yamma.
“A madadin mu da ke a wannan kungiyar ta PMAWCA, muna godiya da lokacinku da kuka bayar da kuma irin kwarewar da ku bayar domin kara habaka hada-hadar kasuwanci da kokarin da ku ka yi, domin amfana da albakatun da ke a bangaren tafiyar da harkar sufurin Jiragen Ruwa a yankin, “ Inji Dantsoho.
“Duba da irin sakonnin da kuka gabatar a wajen taron, musamman a zaman taron na musamman hakan ya nuna cewa, a shirye kuke wajen kara kwarin Guiwar fannin na sufurin Jiragen Ruwa da ke a yankin, “ A cewar Shugaban.
A cewarsa, yanayin tasawirar kasa da kuma tattalin arzkin da ke a yankin a zahirance, hakan ya nuna bukatar karfafa hadin kai, musamman domin a kara bunkasa fannin wajen samar da kyakyawan yanayi, tamkar na fadin duniya.
Dantsoho ya kuma nuna jin dadinsa ga Gwamnati da daukacin alummar Jamhiriyar ta Kongo kan karbar bakuncin taron tare da yabawa Sakatare Janar na kungiyar ta PMAWCA, Mista Koffi Jean Marie da kuma tawagar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Pointe-Noire da sauran abokan hadaka.
Kazalika, ya yaba da kokarin da Darakta Janar na He further da kuma Babban Shugaba da sauran mambobi na Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a yankin kan gudunmawar da suka bayar.
Dantsoho ya kuma bukaci da a ci gaba da yin hadaka, domin a kara ciyar da fannib gaba.
An kirkiro da kungiyar ta PMAWCA a watan Okutobar shekarar 1972 a karkashin Hukumar kula da tattalin arziki na Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Freetown, na kasar Sierra Leone.
Kungiyar ta kunshi Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a Afirka ta Yamma wadda kuma ta yadu, zuwa kasar Mauritania, har zuwa kasar Angola.
Kazalika, babbar manufar kungiyar shi ne, kara karfafa ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa da kara samar da kayan aiki a tsakanin ‘ya’yan kungiyar da ke a yankin, musaman domin a bunkasa tattalin azrki da ke a yankin.
Aikin Sabunta Tashoshin Jiragen Ruwa Na Warri Da Koko Za Su Bunkasa Kasuwanci A Nijeriya—NPA
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta alakanta aikin sabunta Tashoshin Jiragen Ruwa na garin Warri da Koko, da ke a jihar Delta, a matsayin wani mataki, na kara gina kasar.
NPA ta kuma yi alkwarin mayar da hada-hadar kasuwanci a Tashoshin, zuwa na bai daya.
Hakan na kunshe ne, a cikin wani kundin tsari da Jaridar The Guardian ta samu.
Hukumar ta ce, aikin zai kasance, tamkar an bude wani sabon babi ne, na samar da damar a yankin.
A cewar NPA, manufar shi ne, domin a maganace cunkoson da ake samu a Tashoshin Jiragen Ruwa na jihar Legas, musamman duba da cewa, Tashoshin na jihar Delta yadda aka tsara su, za su samar da sauki ga yankin Kudu Maso Kudu da Yankin Arewa ta Tsakiya
Baya ga kara habaka hjanyoyin Ruwa na jihar ta Delta zuwa samar da hanyoyin gudanar da hada-hadar kasuwanci aikin na sabuntawar, zai bai wa sauran alumomin damar amfana da aikin.
Wani bincike da Jaridar ta The Guardian ta gudanar, ya nuna yadda aikin sabuntawar zai kara bunkasa ayyukan NPA.
Bisa irin kayan aikin da NPA ke da su, sun nuna cewa, Jiragen Ruwa za su iya sauke kayan da nauyinsu, ya kai tan 293,013 a Tashoshin na jihar Delta, wanda hakan ya kai kaso 10.7 a cikin dari, na yawan hada-hadar da a iya yi, a Tashoshin na Delta.
Ayyukan da NPA ke ci gaba da aiwatarwa abu ne a zahirance, ba wai tatsuniya ba.
Aikin yashe hanyoyin Ruwa na Escrabos da sabunta Tashoshin isar da sakon kota kwana da sanya kayan tsaro a SPB Likoro, wani abu ne, da ke nuna irin kwararran matakan da aka dauka domin karfafa gudanar da ayyuka.
Kazalika, Hukumar ta NPA, ta kara jaddada bai wa masu son zuba hannun jari a fannin, kwarin Guiwa ta hanyar tabbatar da ana bin ka’ida da zauka matakan da suka kamata a Tashoshin na jihar Delta














