Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ce alkaluman yawan abubuwa da aka saya da ba na bangaren kere-kere ba, sun tsaya kan 49 a watan Agusta, babu sauyi daga yadda suka kasance a watan Yuli.
Alkaluman harkokin kasuwanci a bangaren samar da hidimomi sun tsaya kan 49.3 a watan Agusta, su ma ba su sauya ba daga na watan Yuli.
Idan aka yi la’akari da bangarori daban-daban, harkokin kasuwanci a bangaren hidimomin aika sakonni da sadarwa da yada labarai da talabijin da na sadarwar tauraron dan Adam da intanet da manhaja da fasahar sadarwa, duk sun kasance sama da 55, wadanda ke nuna karuwar yawan harkokin.Ana sa ran alkaluman harkokin kasuwanci a bangaren bayar da hidimomi a watan Agusta su tsaya kan 55.5, inda ake hasashen samun tagomashi a kasuwa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














