A daidai lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai SCO na shekara ta 2026 da kuma ziyarar aiki a Kyrgyzstan, a jiya 30 ga watan Agusta, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG tare da kamfanin gidan rediyo da talabijin na kasar Kyrgyzstan sun shirya taron musayar al’adu na kasashen kungiyar SCO na 2026 a birnin Bishkek, hedkwatar kasar.
Shugaban Kyrgyzstan Sadyr Japarov ya aika da sakon taya murna, tare da fatan samun sakamako mai yawa a yayin taron. Manyan baki sama da 100 daga kasashen kungiyar a fannoni kamar siyasa, tattalin arziki, al’adu da kafafen yada labarai da sauransu sun halarci taron.A yayin taron, shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, a kullum CMG yana aiwatar da “ruhin Shanghai”, tare da hadin gwiwa da kafafen yada labarai na kasashen kungiyar don gina tsarin hadin gwiwa.
Kuma CMG yana fatan yin amfani da wannan dama tare da kafafen yada labarai na kasashen kungiyar, don kara bullo da hanyoyin watsa labarai da zurfafa hadin gwiwa, tare da kai musayar al’adu na kasashen kungiyar zuwa wani sabon mataki, da kuma kafa kyakkyawar makomar bil-Adam ta bai daya bisa “ruhin Shanghai”. (Amina Xu)














