Mutane biyu sun rasa rayukansu bayan ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliya a wasu sassan birnin Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.
An bayyana sunayen mamatan da Isa Haruna, mai shekaru 38, jami’in tsaro wanda aka fi sani da Mallam Matari, da kuma Abba Kyari mai shekaru 18, wanda rahotanni suka ce ya nutse a yankin Pompomari.
A cewar hukumar, ambaliyar ta faru ne a unguwannin Malari, Pompomari da sauran yankunan da ke makwabtaka da su bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi da safiyar ranar Litinin.
SEMA ta ce tawagar bincike da ceto ta hukumar, tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Yobe, sun garzaya wurin bayan samun kiran gaggawa, amma sun tarar da mutanen biyu sun riga sun rasu.
Hukumar ta yi kira ga al’umma da su guji zirga-zirga, wasa ko tuki a kan hanyoyin da ambaliya ta mamaye, magudanan ruwa da sauran hanyoyin ruwa domin kauce wa haɗari.














