Wani bincike na shekara-shekara da Cibiyar Bincike ta Pew ta Amurka ta gudanar kwanan nan, ya nuna cewa, a cikin kasashe da yankuna 27 dake cikin 36 da aka gudanar da binciken, masu bayyana ra’ayoyi sun nuna sha’awarsu ga Sin fiye da Amurka.
Shafin yanar gizo na New York Times ya lura cewa sakamakon binciken da cibiyar Pew ta yi, ya nuna kokarin da Sin ke yi na fadada karfinta a fannin al’adu. Rahoton ya nuna cewa, Sin ta karfafa dangantakar tattalin arziki da tsaro da kasashe kamar Brazil da Peru, kuma ta aiwatar da manufar soke harajin kwastam ga dukkan kasashen Afirka masu huldar diflomasiyya da ita.
Wadannan duk dalilai ne da ke haifar da karuwar karbuwar da take samu a duniya.Bugu da kari, shafin yanar gizo na Japan Times ya nuna cewa, tsarin tattaunawar Sin na goyon bayan hadin gwiwa da samun cin nasara tare, kuma yana neman gyara rashin daidaito a tsarin kasa da kasa, akasin Amurka da ke nuna gamsuwa da kuma kiyaye yanayi na rashin daidaito.(Safiyah Ma)














