Gwamnatin Tarayya ta fara raba tan 12,000 na kayan abinci da wasu kayan da ba na abinci ba a jihohin da ambaliyar ruwa ta addabe su.
A ranar Juma’a aka kai wa Jihar Anambra wasu kayan da ba na abinci ba irin su tabarmin roba 7,350, gidan sauro 1,000, katan 600 na sabulun wanka, yadikan shadda 2,500 (kowanne yadi 5), sababbin tufafi na yara guda 1,000, sababbin tufafi na mata 1,000, da sababbin tufafi na maza 1,000.
Haka kuma za a kai wa jihar kayan abinci da su ka haɗa da buhun shinkafa 1,400, buhun wake 1,400 mai awon kilo 10, buhun masara 1,400 mai awon kilo 10, buhun gishiri 75 (awon kilo 20), jarkar man girki 75 (awon lita 20), katan 100 na magi da sauran su, da katan 75 na tumatirin kwali (sacat 50 cikin kowane katan).
Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji Da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana wannan hoɓɓasan a jawabin ta a taron Ranar Rage Aukuwar Bala’o’i ta Duniya ta bana (2022 International Day for Disaster Risk Reduction) wanda aka yi a Abuja a ranar Juma’a.
Ministar, wadda ta samu wakilcin Daraktan Harkokin Agaji a ma’aikatar ta, Alhaji Ali Grema, ta ce ana ƙoƙarin a ƙara azama wajen tunkarar matsalolin ambaliya a ƙasar nan.
Ta ce: “Duk dai ku na sane da ambaliya mai yawan gaske ta ke ta ragargazar jihohi da ƙananan hukumomi da garuruwa da dama a Nijeriya. Girman ɓarnar wannan ambaliya a ƙasar nan za a iya kwatanta shi ne kawai da ambaliyar da ta auku a cikin shekarar 2012.
“An yi asarar rayukan sama da mutum 500, kuma sama da mutum miliyan 1.4 abin ya shafa, kimanin gidaje 90,000 sun ruguje ko sashen su ya lalace, kuma bala’in na ci gaba.
“Haka kuma dubban hektocin gonaki sun lalace wanda hakan ya haifar da fargabar illata samar da abinci a ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan jama’a a Afrika. Wannan babban lamari ya shafi jihohi 27 a cikin jihohi 36 da Gundumar Birnin Tarayya da ake da su.
“A yayin da mu ke juyayin wannan yanayi na ambaliya a Nijeriya, ya kamata mu mai da hankali ga Cikakken Tsarin Rage Bala’i na 2022 (Inclusive Disaster Risk Reduction, IDDRR). Duk da yake ba za mu tsaya ɗora laifin kan wane ko wane ba, ya kamata ku amince da gaskiyar cewa dukkan mu mun samu isasshen gargaɗi kuma mun yi faɗakarwa da wuri.
“Sai dai, tilas ne jama’a su fahimci cewa kowane bala’i ya na faruwa ne a garuruwa kuma dole su riƙa ɗaukar rahotanni kan yanayi da gargaɗin kafin faruwar ambaliya da aka bayar da gaske.
“Ba za mu iya magance aukuwar ambaliya kwata-kwata ba amma za mu iya kare lafiyar jama’a. Haƙƙin yin hakan na mu duka ne.”
Ministar ta bayyana cewa ma’aikatar ta da dukkan masu ruwa da tsaki su na nan su na aikin aiwatar da Tsarin Agajin Gaggawa Ga Ambaliya na Ƙasa (National Flood Emergency Preparedness and Response Plan) wanda Majalisar Gudanarwa ta Tarayya ta amince da shi kwanan nan.
Hajiya Sadiya ta ce: “Tsarin ya gindaya wa dukkan jihohi da ƙananan hukumomi da ma gidaje da garuruwa da ƙungiyoyin sa ido ainihin aiki da kuma haƙƙin da ya rataya a wuyan kowannen su.
“Wannan ma’aikatar ta ɗauki aikin hana aukuwar mace-mace da rasa rayuka a lokacin aukuwar bala’i wanda ake ba da gargaɗi tun kafin faruwar sa kuma ya ke aukuwa a kowace shekara da muhimmanci.”
A wata hira da aka yi da shi, Darakta-Janar na Hukumar Agajin Gaggawa (NEMA), Mustapha Habib Ahmed, shi ma ya ba da tabbacin cewa an fara raba kayan agaji a sauran jihohi domin a rage wa mutanen da bala’in ambaliya ya shafa a jihohi 36 da Gundumar Birnin Tarayya.
Ya ce an fara rabon kayan ne daga Rumbun Musamman na Ƙasa ga mabuƙata a dukkan jihohi bisa amincewar Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya ce: “NEMA ta riga ta kai kayan agaji ga jihohi da dama kuma ta miƙa su ga gwamnatocin jihohi daban-daban domin su raba wa mutanen da abin ya shafa.
“Mu na tabbatar wa da sauran jihohin da ba su karɓi nasu kayan agajin ba cewa kwanan nan za a gama kai wa nasu jihohin a cikin ƙarshen wannan makon. Ana ci gaba da ƙoƙarin tunkarar matsalolin da ake fama da su a lokacin kai kayan saboda yanayin hanyoyin da ambaliyar ruwan ta mamaye.
“Girman bala’in ambaliyar a faɗin ƙasar nan babba ne matuƙa. A yayin da sama da rayuka 500 su ka salwanta, an yi asarar gidaje da gonaki da dama, sannan tilas ɗimbin mutane sun bar gidajen su a wuraren da bala’in ya fi ta’azzara.”