ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Gano Jirgi Mara Matuƙi Da Ake Zargin Masu Laifi Na Amfani Da Shi A Iyakokin Kano

by Sadiq
6 hours ago

Rundunar ’yansandan jihar Kano ta gano wani jirgi mara matuƙi da ake zargin masu aikata laifuka ne ke amfani da shi.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an gano jirgin ne yayin da jami’an ’yansanda ke gudanar da samame a yankunan da ke iyakar jihar.

Ya ce jami’an sun gano jirgin a wani daji da ke Tarau, a cikin ƙaramar hukumar Bebeji ta jihar Kano.

ADVERTISEMENT

A yanzu haka, ƙwararru na binciken jirgin domin gano irin abubuwan da ke cikinsa da kuma abin da ake amfani da shi.

A wani samame kuma, ’yansandan sun kama wani mutum mai shekara 35 da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

LABARAI MASU NASABA

Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

Tinubu Ya Yi Wa Nijeriya Kyakkyawan Tanadi – Masari

Kiyawa ya ce wanda aka kama na zaune a Kunkumi, ƙaramar hukumar Maƙarfi a jihar Kaduna, kuma ana zarginsa da kasancewa cikin wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ke da hannu wajen garkuwa, fashi da makami da satar shanu a Kano, Katsina da Kaduna.

Ya ce bincike ya kai ga kama wani mutum da ke zaune a Kwanar Ɗangora a Kano, wanda ake zargi da taimaka wa ƙungiyar wajen shirya yadda za a yi garkuwa da mutane.

A cewar ’yansandan, waɗanda ake zargin sun taɓa yin garkuwa da wata mata, inda suka karɓi Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa.

Haka kuma, ana zargin sun sace wani mutum a garin Gwarzo, suka kai shi jihar Kaduna, inda suka riƙe shi har sai da iyalansa suka biya kuɗin fansa.

Kakakin ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin.

Ya tabbatar da cewa za a gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu bayan kammala bincike.

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗaga Albashin Sojoji Daga Naira 49,000 Zuwa Naira 100,000 – Ministan Tsaro
Manyan Labarai

Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

September 23, 2026
Tinubu Ya Yi Wa Nijeriya Kyakkyawan Tanadi – Masari
Manyan Labarai

Tinubu Ya Yi Wa Nijeriya Kyakkyawan Tanadi – Masari

September 23, 2026
Har Yanzu Tinubu Ne Ke Shugabancin Nijeriya Daga Waje – Akpabio
Manyan Labarai

Har Yanzu Tinubu Ne Ke Shugabancin Nijeriya Daga Waje – Akpabio

September 23, 2026
Next Post
Yadda Fasahohin Noma Na Sin Ke Canza Rayuwar Manoman Afirka

Yadda Fasahohin Noma Na Sin Ke Canza Rayuwar Manoman Afirka

LABARAI MASU NASABA

Sultan

Kada Ku Ɗauki Nauyin Aikin Hajji Da Kuɗaɗen Da Aka Sace — Sultan Ga ’Yan Siyasa

September 23, 2026
Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

September 23, 2026
Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara N10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara N10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

September 23, 2026
Sin Ta Yi Bikin Karrama ’Yan Sama Jannati Na Kumbunan Shenzhou-20 Da Shenzhou-21

Sin Ta Yi Bikin Karrama ’Yan Sama Jannati Na Kumbunan Shenzhou-20 Da Shenzhou-21

September 23, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ɗaga Albashin Sojoji Daga Naira 49,000 Zuwa Naira 100,000 – Ministan Tsaro

Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

September 23, 2026
Yadda Fasahohin Noma Na Sin Ke Canza Rayuwar Manoman Afirka

Yadda Fasahohin Noma Na Sin Ke Canza Rayuwar Manoman Afirka

September 23, 2026
An Gano Jirgi Mara Matuƙi Da Ake Zargin Masu Laifi Na Amfani Da Shi A Iyakokin Kano

An Gano Jirgi Mara Matuƙi Da Ake Zargin Masu Laifi Na Amfani Da Shi A Iyakokin Kano

September 23, 2026
TMG Ta Buƙaci Atiku Da Obi Su Haɗa Kai Don Kayar Da Tinubu A 2027

TMG Ta Buƙaci Atiku Da Obi Su Haɗa Kai Don Kayar Da Tinubu A 2027

September 23, 2026
Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Amurka Don Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar

Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Amurka Don Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar

September 23, 2026
Tinubu Ya Yi Wa Nijeriya Kyakkyawan Tanadi – Masari

Tinubu Ya Yi Wa Nijeriya Kyakkyawan Tanadi – Masari

September 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.