An gudanar da dandalin tattaunawa na jama’a na WTO na 2026 na kwanaki uku a birnin Geneva na Switzerland. A yayin taron wanda aka yi kwanan nan, an nuna jerin shirye shiryen gabatar da al’adun kasar Sin mai taken “Damar da za a samu a Sin: Kirkira da makoma ta bai daya”.
A jawabin da ta gabatar a wurin taron, Li Yongjie wakiliyar dindindin ta Sin dake WTO, ta bayyana cewa a bana ake cika shekaru 25 da Sin ta shiga cikin WTO, tana mai fatan cewa ruhin “daidaita bambancin ra’ayi” da “rike ginshikai yayin da ake neman kirkire-kirkire”, wanda shirye-shiryen gabatar da al’adun suka samar, zai sa mutane su yi hasashen wata makomar tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban wadda take a bude kuma mai hadin kai da juriya, ta yadda WTO za ta samu damar karfafa makomar dukkan membobinta.
Babbar daraktar WTO Ngozi Okonjo-Iweala ta gode wa Sin bisa karbar bakuncin jerin shirye-shiryen na gabatar da al’adu, tana mai cewa musayar al’adu tana gabatar da ra’ayi na musammam kan ciniki da kuma dunkulewar kasa da kasa.(Safiyah Ma)














