Fu Cong, zaunannen wakilin Sin da ke MDD, ya bayyana cewa ana gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD ne don kiyaye zaman lafiya kana sun kasance matsayin ingantattun kayan aikin kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya.
Ya ce a lokacin da yake ba da umarni, ya kamata kwamitin sulhun ya inganta ayyuka da tabbatar da cewa albarkatu sun dace da abun da ake bukata, a lokaci guda kuma, ya kamata ya karfafa hadin gwiwa don gina karfin kasashe wajen kiyaye zaman lafiya.
Fu Cong ya bayana hakan ne a muhawarar da kwamitin sulhun ya gudanar kan ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD a jiya Jumma’a.
Fu Cong ya kara da cewa, Sin na fatan inganta ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD ta yadda za su kasance masu amfani da inganci da kuma dorewa, da hadin kai tsakanin dukkan bangarori karkashin jagorancin shawarar tsarin inganta shugabancin duniya, ta yadda za a ba da gudummawa sosai ga kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya.(Safiyah Ma)














