Shugaba Bola Tinubu ya ce amfani da motoci masu amfani da CNG da lantarki ya rage kuɗin sufuri da tsakanin kashi 31 zuwa 83 cikin 100 a wasu hanyoyin jihohi bakwai da Abuja.
Tinubu ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Asabar, inda ya ce tuni ’yan Nijeriya suka fara amfana da ragin kuɗin sufuri.
A Borno, kuɗin da masu motocin haya da ke amfani da CNG da lantarki ya ragu daga naira 100 zuwa 50, daga naira 600 zuwa 300.
A Oyo, kuɗin mota daga Legas zuwa Ibadan ya ragu daga kusa naira 8,000 zuwa naira 3,200.
A Filato kuma, motocin da gwamnati ke tallafawa suna karɓar naira 200 maimakon sama da naira 500.
A Enugu, kuɗin mota daga Enugu zuwa Nsukka ya ragu daga naira 2,500 zuwa naira 1,500, yayin da na hanyar Suleja zuwa Abuja ya koma naira 550 daga kusan naira 800.
A Abia kuma, an tura motoci masu amfani da lantarki 40, inda gwamnati ke tallafa wa kuɗin sufuri da kashi 50 cikin 100.
A Abuja, motocin haya da aka mayar da su CNG suna bai wa fasinjoji rangwamen kashi 40 cikin 100 a wasu hanyoyi.
Misali, kuɗin mota daga Area 1 zuwa Gwagwalada ya ragu daga naira 1,500 zuwa naira 900.
Tinubu ya ce shirin na da nufin rage kuɗin sufuri da kuma rage tasirin tashin farashin man fetur.














