A kwanan baya, shugaban majalisar dokokin kasar Angola, Mista Adao Almeida, ya yi ziyarar aiki a kasar Sin. Yayin da yake hira da wakilin kafar CMG, Mista Almeida ya ce, kasar Sin tana da shugaba mai hangen nesa, wanda yake kulawa da al’ummar kasar cikin tsanake. A cewar Almeida, shugaba Xi Jinping na kasar Sin yana da wasu halaye na musamman, kamar dora matukar muhimmanci kan ci gaban tattalin arziki, da fahimtar ainihin kalubalolin da kasar Sin da sauran kasashe daban daban suke fuskanta, da kokarin neman bakin zaren warware matsalolin.
A lokacin da ya ambaci shawarwari guda 4 da shugaba Xi ya gabatar a kokarin daidaita al’amuran duniya, Mista Almeida ya ce, wadannan shawarwari suna da amfani ga yunkurin kafa tsarin kasancewar bangarori masu fada-a-ji da yawa a duniya, ta yadda za a samar da wani dandali na tattaunawa tsakanin kasashe daban daban, don tsara wasu ka’idoji na bai daya da za su biya bukatun daidaita al’amura, da ba da damar kara dora muhimmanci kan hadin kan al’ummun sassan duniya, maimakon kebabbun kasashe marasa alaka a tsakaninsu.
Kana Mista Almeida ya bayyana kasar Sin a matsayin wata babbar kasa, wadda ke taka rawar gani a fannin zamanantar da al’umma, da sauya tsarin masana’antu zuwa na dijital. A cewarsa, dalilin da ya sa kasar Sin samun nasara a fannin raya kasa, shi ne tsarinta na siyasa mai inganci, da cikakken tunanin da ake da shi a fannin raya kasa, da yadda ake aiwatar da manufofi yadda ake bukata. Ban da haka, ingantaccen tsarin kasar na sanya ido kan harkoki daban daban, shi ma ya samar da gudunmowa sosai.
Har ila yau, Mista Almeida ya ambaci hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Sin da Angola ta fuskar tattalin arziki. Ya ce akwai daruruwan kamfanonin kasar Sin da suke aiwatar da harkokinsu a kasar Angola, wadanda suka zuba jari, gami da kafa rassa a kasar. Kana wasu daga cikinsu sun kwashe shekaru da dama suna kokarin raya harkokinsu a kasar Angola. Ban da haka, dimbin kamfanonin kasar Sin na taimaka wa kasar Angola a yunkurinta na raya sassa daban daban na tsarin tattalin arziki. (Bello Wang)














