Mataimakin firaministan gwamnatin kasar Sin He Lifeng, da sakataren kudi na Amurka Scott Bessent, da wakilin kasuwanci na kasar Jamieson Greer, wadanda suke jagoranci tuntuba tsakanin Sin da Amurka kan harkokin tattalin arziki da kasuwanci, sun gudanar da tattaunawar tattalin arziki da kasuwanci a New York na Amurka a jiya Lahadi.
Bangarorin biyu, sun yi tattaunawa mai zurfi cikin hakikannin hali, da fatan samun ci gaba na a zo a gani, kan aiwatar da yarjejeniyoyin tattaunawar tattalin arziki da kasuwanci da suka gabata, da habaka cinikayya, da zuba jari tsakaninsu, da sauran muhimman batutuwan tattalin arziki da kasuwanci da suka shafi bangarorin biyu, bisa jagorancin matsayar da shugabannin kasashen biyu suka kafa, tare da nacewa ga ka’idojin girmama juna, da zama tare cikin kwanciyar hankali, da hadin gwiwa mai amfani ga kowa.Ban da wannan kuma, sun gudanar da tattaunawa kan batutuwan da suka shafi fasahar AI da abubuwan masu nasaba da hakan. (Amina Xu)













