A yau Lahadi aka kammala gasar wasanni ta nahiyar Asiya ta Aichi-Nagoya, bayan shafe makonni 2 ana fafatawa, inda Sin ta kankane teburin lambar yabo ta zinare, karo na 12 a jere.
Kasar Sin ta kammala da lambobin zinare 169 da na azurfa 89 sai tagulla 83, karo na farko da ta nuna irin wannan bajinta a gasar ta nahiyar Asiya da aka yi a ketare.
Kasar Japan ce ta zo a matsayi na 2 da zinare 83 da azurfa 95 sai tagulla 91, sai Koriya ta Kudu da ta rufa mata baya da zinare 39 da azurfa 43 da tagulla 68.
‘Yan wasa da jami’ai sama da 17,000 daga kasashe da yankuna 45 ne suka shiga gasar yayin da aka karya matsayin bajinta na duniya fiye da 50.
Dan wasan tsere na kasar Thailand Puripol Boonson da ‘yar wasan ninkaya ta Sin Yu Zidi ne suka samu karramawar ‘yan wasa mafi daraja a gasar, a ajin maza da na mata.
An mika tutar gasar daga hannun Aichi-Nagoya zuwa birnin Doha, da zai karbi bakuncin gasar wasannin ta nahiyar Asiya karo na 21.(Fa’iza Mustapha)














