Shugaba Bola Tinubu, ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da karɓo bashin ƙasashen waje na kusan dala biliyan 20.5 da kuma Yuro biliyan 1.04 domin gudanar da muhimman ayyuka a ƙarƙashin shirin rancen kuɗin Gwamnatin Tarayya na shekarun 2026 zuwa 2027.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne, ya karanta wasiƙar buƙatar shugaban ƙasar yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Ana sa ran za a yi amfani da kuɗin wajen ayyukan samar da wutar lantarki, sufuri, kiwon lafiya, ilimi, noma, samar da ruwa, tsaro da samar da ayyukan yi.
Tinubu ya ce kuɗin za su taimaka wajen magance ƙarancin ababen more rayuwa a Nijeriya, rage talauci, samar da ayyukan yi da kuma inganta wadatar abinci.
Ya ƙara da cewa an gudanar da bincike kan ayyukan da aka zaɓa domin tabbatar da cewa za su amfani al’umma yadda ya kamata.
Shugaban ƙasar ya ce karɓar bashin ƙasashen waje ya zama dole saboda yawan kuɗin da ake buƙata wajen inganta ababen more rayuwa da tallafa wa ɓangaren tattalin arziƙin ƙasar.
Majalisar Dattawan ta miƙa buƙatar ga kwamitinta mai kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje, ƙarƙashin jagorancin Sanata Haruna Manu, domin yin nazari.
Kwamitin zai tantance shirin da yadda ya dace da tsare-tsaren karɓar bashi da ake da su kafin majalisar ta ɗauki mataki na gaba.














