Ɗaliban Makarantar Sunflower da ke Jihar Kano sun lashe gasar ɗalibai ta ƙasa ta shekarar 2026, wadda ƙungiyar Junior Achievement Nigeria ta shirya.
Ƙungiyar ɗaliban mai suna AgroLens Technologies ta ƙirƙiri manhajar wayar salula mai suna AgroLens AI, wadda ke taimaka wa manoma gano cututtukan amfanin gona da ƙwari, tare da ba su shawarar maganin da ya dace su yi amfani da shi.
Manhajar tana kuma nuna farashin amfanin gona a kasuwa, haɗa manoma da masu sayen amfanin gonarsu, da kuma ba su bayanai kan yadda za su samu bashi kuɗi don yin noma.
Manhajar tana aiki da harsunan Turanci, Hausa, Yarbanci, Inyamuranci da Pidgin.
Ɗaliban sun lashe kyautar dala 250 da kuma damar tafiya zuwa birnin Cape Town na Afirka ta Kudu, inda za su wakilci Nijeriya a gasar ɗalibai ta Afirka.
Sun kuma samu kyaututtuka saboda ƙirƙirar sabuwar fasaha da kuma ƙwarewa wajen gudanar da ayyukansu.
Wannan nasara ita ce karo na uku a jere da Kano ke lashe gasar ta ƙasa.














