ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, October 27, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kamafanin Simintin Dangote Ya Ƙara Kaimi Wajen Inganta Ayyukan Direbobinsa A Faɗin Afirka

by Rabi'u Ali Indabawa
57 minutes ago

Kamfanin Smintin Dangote, babban kamfanin samar da siminti a Afirka, ya ƙara ƙaimi wajen inganta tsaron hanya ta fannin ƙarfafa matakan wayar da kan direbobi, kwarewarsu da kuma bin ƙa’idojin aiki mafi inganci a dukkan ayyukansa da ke faɗin Afirka.

Da yake magana a taron horar da direbobi kan tsaro na shekarar 2026, wanda aka gudanar a masana’antar Kamfanin Simintin Dangote da ke Obajana, Jihar Kogi, Manajan Darakta na Rukunin Kamfanin Smintin Dangote, Mista Arvind Pathak, ya ce dole ne direbobi su rika “Tunanin Tsaro da Aiki Cikin Kiyayewa” a dukkan ayyukan kamfanin da ke Afirka.

Ya sake jaddada ƙudurin kamfanin na tabbatar da tsaro da walwalar direbobinsa, inda ya buƙace su da su ba da fifiko ga tuƙi cikin aminci tare da tabbatar da cewa sun koma gida lafiya bayan kowace tafiya.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, Kamfanin Simintin na Dangote, a matsayinsa na babban kamfanin samar da siminti a Nijeriya da Afirka, yana ba da muhimmanci sosai ga ingancin kayayyakinsa, yayin da direbobinsa ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa kayayyakin sun isa ga abokan ciniki cikin aminci da inganci.

Pathak ya jaddada cewa babu wani aikin kai kaya na kasuwanci da ya kai darajar rasa ran ɗan ‘Adam, yana mai bayyana cewa tsaron direbobi ya fi muhimmanci fiye da manufofin gudanar da aiki da kuma la’akari da kasuwanci.

LABARAI MASU NASABA

Ƙungiyar Ansaru Ta Ɗauki Alhakin Kashe Yahaya Masussuka A Katsina

Ba Don Taimakon Tinubu Ba, Da Buhari Bai Zama Shugaban Ƙasa Ba – Abba Bichi

Taron, wanda aka gudanar ƙarƙashin taken “Tunanin Tsaro, Aiki Cikin Tsaro,” ya haɗa direbobi, da ma’aikatan sufuri da wakilan gudanarwar kamfanin domin inganta tuƙi cikin ɗaukar nauyi, da tattauna matsalolin walwala da kuma karfafa al’adun tsaro a dukkan ayyukan sufuri na kamfanin.

Da yake jawabi ga mahalarta, Pathak ya tunatar da direbobin cewa su ne wakilan kamfanin Dangote a manyan hanyoyin ƙasar, kuma suna da alhakin kare rayukansu da na sauran masu amfani da hanya.“Duk lokacin da kuka hau kan sitiyari, ba kaya kawai kuke ɗauke da su ba. Kuna ɗauke da martabar wannan kamfani, amincewar sauran masu amfani da hanya, kuma mafi muhimmanci, rayuwarku.“Za mu iya maye gurbin babbar mota; amma ba za mu iya maye gurbin ɗan’Adam ba,” in ji shi.

Ya tabbatar wa direbobin cewa kamfanin zai ci gaba da sanya jari a shirye-shiryen da aka tsara domin inganta walwalarsu, da haɓaka kwarewarsu ta sana’a da kuma inganta ayyukan sufuri cikin aminci.

A cewarsa, direbobi na da muhimmiyar rawa wajen ci gaban kamfanin da tsarin rarraba kayayyaki, wanda hakan ya sa tsaro da walwalarsu suka zama abubuwan da kamfanin ke ba da fifiko.“Mun yaba da sadaukarwar da kuke yi a kowace rana domin tabbatar da ci gaba da ayyukan kasuwancinmu. Wannan ne ya sa muka ƙuduri aniyar ba ku kayan aiki da horon da za su taimaka muku wajen aiki cikin aminci, tare da sauraron damuwarku da inganta walwalarku.“Idan direbobinmu suna cikin aminci, ayyukanmu za su fi karfi, al’ummominmu kuma za su fi kasancewa cikin tsaro,” in ji Pathak.

Ya buƙaci direbobin da su guji wuce gona da iri wajen gudu, tuƙi bayan gajiya da sauran halayen tuki masu haɗari, yana mai jaddada cewa ya kamata a auna kwarewar direba ta hanyar isa wurin da ake nufi cikin aminci, ba ta hanyar saurin kammala tafiya ba.

Shugaban Kamfanin Simintin Dangote ya shawarci direbobin da su riƙa tsayawa su huta duk lokacin da suka ji gajiya, tare da guje wa ɗaukar haɗarin da ba dole ba a kan hanya.“Ina son kowane direba ya tuna da wata muhimmiyar ƙa’ida: idan ka gaji, ka tsaya ka huta. Idan wani yanayi ya bayyana ba shi da aminci, kada ka yi gangancin ɗaukar haɗari.“Manufar ba wai kawai ka isa inda za ka je ba ce; manufar ita ce ka koma gida lafiya ga iyalinka,” a cewarsa.

Shugaban Sufuri na Kamfanin Simintin Dangote, Murilo Silva, yayin da yake jawabi ga direbobin, ya gargaɗe su kan tuƙin ganganci, tukin da wani ke yi a madadin direban da aka ba shi aiki da sauran ayyukan sufuri marasa aminci, yana mai cewa ba za a lamunci irin waɗannan halaye ba.

Silva ya bukaci direbobin da su ɗauki alhakin ayyukansu da kansu, tare da bayar da gudummawa wajen tabbatar da cewa hanyoyin Nijeriya sun fi aminci ga masu motoci da sauran masu amfani da hanya.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Samar Da Kayayyakin Cikin Gida Na Da Muhimmanci Wajen Ƙarfafa Tattalin Arziki – Dangote
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Dole Afirka Ta Samar Da Hanyoyin Magance Matsalolinta
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja

MASU ALAKA

Ƙungiyar Ansaru Ta Ɗauki Alhakin Kashe Yahaya Masussuka A Katsina
Labarai

Ƙungiyar Ansaru Ta Ɗauki Alhakin Kashe Yahaya Masussuka A Katsina

October 27, 2026
Ba Don Taimakon Tinubu Ba, Da Buhari Bai Zama Shugaban Ƙasa Ba – Abba Bichi
Manyan Labarai

Ba Don Taimakon Tinubu Ba, Da Buhari Bai Zama Shugaban Ƙasa Ba – Abba Bichi

October 27, 2026
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa
Manyan Labarai

Tinubu Ya Nemi Majalisar Dattawa Ta Amince A Karɓo Bashi Daga Ƙasashen Waje Na Dala Biliyan 20.5

October 27, 2026

LABARAI MASU NASABA

Kamafanin Simintin Dangote Ya Ƙara Kaimi Wajen Inganta Ayyukan Direbobinsa A Faɗin Afirka

Kamafanin Simintin Dangote Ya Ƙara Kaimi Wajen Inganta Ayyukan Direbobinsa A Faɗin Afirka

October 27, 2026
Ƙungiyar Ansaru Ta Ɗauki Alhakin Kashe Yahaya Masussuka A Katsina

Ƙungiyar Ansaru Ta Ɗauki Alhakin Kashe Yahaya Masussuka A Katsina

October 27, 2026
Ba Don Taimakon Tinubu Ba, Da Buhari Bai Zama Shugaban Ƙasa Ba – Abba Bichi

Ba Don Taimakon Tinubu Ba, Da Buhari Bai Zama Shugaban Ƙasa Ba – Abba Bichi

October 27, 2026
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Majalisar Dattawa Ta Amince A Karɓo Bashi Daga Ƙasashen Waje Na Dala Biliyan 20.5

October 27, 2026
Sauran Kwanaki Kaɗan A Rufe Neman Tallafin Karatu Na Indomie

Sauran Kwanaki Kaɗan A Rufe Neman Tallafin Karatu Na Indomie

October 27, 2026
Tinubu Ba Shi Da Ƙwarewa Da Lafiyar Da Zai Jagoranci Nijeriya – Obi

Tinubu Ba Shi Da Ƙwarewa Da Lafiyar Da Zai Jagoranci Nijeriya – Obi

October 27, 2026
Shugaban Hisbah Na Bauchi, Aminu Balarabe, Ya Yi Murabus

Shugaban Hisbah Na Bauchi, Aminu Balarabe, Ya Yi Murabus

October 27, 2026
Ɗaliban Kano Sun Lashe Gasar Ƙasa Da Ƙasa Da Manhajar AI Ta Noma

Ɗaliban Kano Sun Lashe Gasar Ƙasa Da Ƙasa Da Manhajar AI Ta Noma

October 27, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Aikin Inganta Wutar Lantarki A Kano Da Katsina

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Aikin Inganta Wutar Lantarki A Kano Da Katsina

October 27, 2026
Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?

Waɗanne Ƙalubale Waɗanda Aka Yi Garkuwa Da Su Suke Fuskanta Bayan Sun Dawo Gida?

October 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.