Jiya ranar 1 ga watan Oktoba, an kunna fitilu masu kyan-gani a husumiyar Burj Khalifa, gini mafi tsawo a duniya, da ke birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, don murnar cikar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin shekaru 77 da kafuwa.
Hoton tutar kasar Sin hade da hasken fitilun sun haska a jikin husumiyar mai tsawon mita 828, inda aka gabatar da wannan gagarumin bikin kunna fitilu masu kyan-gani da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya shirya.
Haka kuma, wannan ne karo na farko da CMG ya gabatar da irin wannan bikin kunna fitilu a yayin murnar zagayowar ranar kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a gini mafi tsawo a duniya. (Murtala Zhang)














