Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara gwajin na’urar BVAS gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Kwamishinan Zaɓe na INEC a jihar Ondo, Mutiu Agboke, ya ce hukumar na ɗaukar matakai domin ganin an gudanar da zaɓe mai cike da ‘yanci, adalci, sahihanci.
Ya ce INEC za ta gudanar da wani zaɓen gwaji a watan Nuwamba, domin tantance shirinta da kuma gano matsalolin da ka iya tasowa kafin ranar zaɓe.
Wannan gwajin zai taimaka wa hukumar wajen gano matsalolin fasaha da na gudanar da zaɓe, tare da yin gyare-gyaren da suka dace kafin babban zaɓen 2027.
Agboke ya kuma ce INEC za ta ƙara wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a domin su fahimci tsarin zaɓe da kuma ƙarfafa musu gwiwar shiga harkar zaɓe.
A wani taro da aka gudanar a Akure, masu ruwa da tsaki sun buƙaci ’yan Nijeriya, musamman matasa, da su ƙara shiga cikin harkokin zaɓe tare da ci gaba da tattaunawa kan yadda za a ƙarfafa dimokuraɗiyya a ƙasar.














