An nada Yusuf Nasidi Nasir a matsayin Talban Barayan Kano, a wani gagarumin bikin nadin sarauta da aka gudanar a fadar Barayan Kano da ke garin Zakirai da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa ta Jihar Kano.
An gudanar da bikin ne a ranar Juma’a, 21 ga Agusta, 2026, a bisa jagorancin Mai Martaba Barayan Kano kuma Hakimin Zakirai, Alhaji Sule Salihi, bisa amincewar Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.
Bikin ya samu halartar manyan baki da suka haɗa da masu riƙe da sarautun gargajiya da ’yan uwa da abokan arziki, da sauran al’umma da suka halarci bikin domin taya sabon Talban Barayan Kano murna.
A yayin bikin, an tabbatar da nadin Yusuf Nasir a matsayin Talban Barayan Kano, inda aka buƙace shi da ya riƙe sarautar bisa gaskiya da amana, tare da ci gaba da kiyaye dokokin addinin Musulunci.
Barayan na Kano, ya buƙaci sabon Talban da ya ci gaba da taimakon al’umma kamar yadda ya saba, tare da kawo wa masarauta duk wani ci gaba da zai taimaka wajen bunƙasa ta, a matsayin hidima ga masarauta da al’umma.
A nasa ɓangaren, Talban Barayan Kano, Yusuf Nasidi Nasir, ya gode wa jama’ar da suka halarci bikin nadin sarautar tasa, tare da nuna godiyarsa bisa addu’o’in da suka yi masa na fatan alheri.
Ya kuma bayyana godiyarsa ga Masarautar Zakirai da Masarautar Kano da dukkan waɗanda suka taka rawa wajen ganin an gudanar da bikin cikin nasara.














