Cibiyar Zaki’s GEM da ke rajin fafutukar kwato wa ‘ya’ya mata da maza hakkokinsu da kuma haror da su sana’o’i hannu na zamani domin samu su dogaro da kansu ta bayyana cewar, “daga farkon wannan shekara ta 2020 zuwa wannan wata na Dasamba da muke ciki an samu matsalolin cin zarafin ‘ya’ya mata fiye 200 a jihar kebbi wanda a cikin su, Cibiyar Zaki’s GEM ta dauki nauyin mata 45 da ke fustantar matsalar cin zarafin a kotutuka daban daban domin tabbatar da cewa ba a dan ne musu hakkokinsu ba, inji Ambasada Nafisa Abubakar Zaki Shugabar Cibiyar Zaki’s GEM yayin da ta gudanar da taron bikin kwanaki goma sha shidda na duniya karo na biyu a jihar ta kebbi da ake yekuwa kan kawo karshen cin zarafin ‘ya’ya mata a jahohin kasashen duniya”.
Wanda ta ce” jihar kebbi bata da yawan kididigar matan da kananan yara da aka ci zarafin su ta hanyar fyade, amma cibiyar Zaki’s GEM tayi hadin gwiwa da hukumomin tsaro, Asibiti da kuma hukumar Hisba domin samun kididigar wanda har yanzu ba a kammala tattara kididigar ba, amma wannan kididigar da na bayyana cikin wadda aka samu ce, inji Shugabar Cibiyar Zaki’s GEM Nafisa Abubakar Zaki”.
An gudanar da wannan bikin ne a dakin gudanar da taro na Ma’aikatar kula da harakokin mata da kuma jinda di na jihar kebbi wato( ministry of women Affairs and social Debelopment) a jiya a Birnin-Kebbi. Inda shgabar ta cibiyar Zaki’s GEM ta kara da cewa” taken bikin wannan shi ne kawo karshen cin zarafin mata da kuma kannan yara a duk fadin jihar kebbi”, ta ce” wannan kididigar yawan matan da aka cin zarafin su mun tattaro ta ne a hannun asibiti, jami’an tsaro da kuma hukumar Hisba a jihar ta kebbi wanda har yanzu ma ba a kammala tattara yawan kididigar matan da ake cin zarafin su, inji Ambasada Nafisa Abubakar Zaki yayin wata zantawa da tayi da manema labaru bayan kammala taron bikin a jiya”.
Ta ci gaba da cewa” cibiyar ta ta Zaki’s GEM tana da hadin gwiwa da Ma’aikatun gwamnatin jihar kebbi, hukumomin jihar, jami’an tsaro da kuma hukumar Hisba har ma da sarakunan gargaji na duk fidn kannan hukumomin Ashirin da daya na jihar ta kebbi domin samun nasarar dakile yawan cin zarafin mata da kuma kananan yara a jihar.
Haka kuma ta godewa Babbar Sakatariyar Ma’aikatar kula da harakokin mata da jinda di Hajiya Aisha Muhammadu Maikurata ga irin gudunmuwa da kuma goyon kan tabbatar da cewa mata a jihar kebbi sun samu ‘yancin su a koda yaushe. Hakazalika ta yabawa matar Gwamnan jihar, Daktar Zainab Shinkafi Bagudu kan bude wata cibiyar sashe da ke kula da mata da kuma kananan yara da aka cin zarafin su, a cikin Babbar Asibitin gwamnatin jihar da ke a garin Kalgo, wannan karamin taimako ba ne, saboda hakan muna godiya sosai.
Daga nan Ambasada Nafisa Abubakar Zaki ta kara godewa sarakunan gargaji na duk fadin jihar kan goyon bayan su wurin gudanar da yekuwa da kuma fadakarwa ga al’ummar kan illolin da ke tattare wurin cin zarafin mata da kuma kananan yara a yankunan su.