Kwamitin wani masallaci a Jihar Bauchi ya sauke Limamin masallacin, Dahiru Abubakar, saboda yi wa Shugaba Bola Tinubu kamfen a lokacin wa’azi da bayan idar da salloli.
Limamin ya ce yana yi wa jama’a wa’azi ne domin su daina ɗora wa Tinubu laifin matsalolin tsaro da tsadar rayuwa, yana mai cewa waɗannan matsaloli suna buƙatar taimakon Allah domin a shawo kansu.
Sai dai shugaban kwamitin masallacin, Imam Abubakar Jibrin, ya ce limamin ya sha yin watsi da gargaɗin da aka yi masa na ka da ya mayar da masallacin wajen harkokin siyasa.
Ya kuma zarge shi da ƙoƙarin sauya sunan masallacin zuwa Masallacin Imam Bola Ahmed Tinubu.
Kwamitin ya bayyana cewa an gina masallacin ne domin bautar Allah, ba domin harkokin siyasa ba.
Ya kuma tabbatar da cewa ba za a mayar da limamin kan muƙaminsa ba.
Jibrin ya ƙara da cewa kwamitin ba ya goyon bayan wani ɗan takarar siyasa, kuma addu’arsu ita ce Allah Ya zaɓa wa Nijeriya shugaba na gari.














