Renaguli Kerman ta taba shiga cikin jerin masu fama da talauci, tare da sauran magidanta kimanin dubu 1. Daga bisani, ita da iyalinta sun kaura daga yankin tsauni na gundumar Kizilsu Kirghiz mai cin gashin kanta dake jihar Xinjiang zuwa garin Tongan na gundumar Zepu dake yankin Kashgar na jihar Xijiang.
Bayan sun kaura, gwamnatin wurin ta dukufa domin tabbatar da yanayin zaman karko da neman hanyoyin wadata jama’a.
A garin Tongan dake kusa da kogin Yarkand, an shafe shekaru biyu wajen kyautata yanayin gonakin da fadinsu ya kai sama da muraba’in eka 800. Bayan samun gonaki masu kyau, sai jama’ar wurin suka fara raya sana’o’in shuke-shuke da kiwon dabbobi.
Sa’an nan, a shekarar 2020, an kawar da garin Tongan daga kangin talauci baki daya, zaman rayuwar al’umma na ci gaba da kyautatuwa. An kuma gina hanyoyi da dama, ta yadda, al’ummomin ke iya samun Karin damammakin neman aikin yi da samun wadata.
Renaguli Kerman ta ce, yanzu, muna da gonaki, da sabbin gidaje, da kantuna, kuma, yaranmu suna iya zuwa makarantu domin koyon ilmi, a nan gaba za su sami aikin yi. Kasarmu ta samar mana da manufofi masu kyau da amfani, ya kamata mu yi amfani da wannan dama wajen kyautata zaman rayuwarmu. Ta kuma kara da cewa, ta gamsu sosai, kuma tana sa ran ginuwar wata makoma mai haske. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)