• English
  • Business News
Friday, October 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
2 hours ago
in Dausayin Musulunci
0
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mun gode wa Allah, Mun gode wa Allah da ya sake tara mu a cikin wannan shafi mai albarka. Har yau dai, muna ci gaba da murnar cikar Haihuwar Manzon Allah (SAW) shekara 1500, wajibi ne mu yi godiya ga Allah. Domin Manzon Allah (SAW) shi ne Annabin annabawa (SAW) Ma’aikin ma’aika, malamin malamai (SAW) shugaban masu tsoron Allah da masoya Allah da masu bautar Allah (SAW).

Wani malami daga cikin Falasifawa wadanda suka sa kwakwalwa suka yi tunani suka gwada abubuwa suka tankade suka rairaye suka fadi abin da gaskiya ta nuna masu, ba ruwansu da wani bangare na addini, bare su ji tsoron fadar duk wata gaskiya, kada a ce sun taba addinin wani, ba ruwansu da bangaren wata jama’a, su hadimar ilimi ne, ilimi suke yi wa hidima. Su in ilimi ya yadda da wani abu sun gwada sun gani to ko zai zama a bakin ransu za su fada, za su fito da abin da wannan ilimi ya ba su.

  • Sadaukantaka, Kunya Da Kawar Da Kai Na Annabi Muhammadu (SAW)
  • Kadan Daga Hakuri Da Yafiya Da Rangwamen Annabi (SAW)

Amma wanda yake karkashin wani ra’ayi ko karkashin wani addini ko wata akida zai ga wani abu in ya fada zai ga kamar addininsa bai yadda da shi ba ko jama’arsa ba su yadda da shi ba, saboda haka sai su ji tsoron fadar gaskiya. Amma su falasifawa suna maganar hankali, Allah ya ba su hankali suna gwada abun da hankali kuma Allah ya basu ilimi suna gwada abun da ilimi.

Shi wannan ya gwada mazaje ya gwada Annabawa da aka fada, ya gwada duk wasu mazaje da suka yi tashe duk ga baki daya har ya zo ya gwada Annabi (SAW), ya dora shi kan sikeli irin nashi, ta ko wanne bangare, sai ya cimma matsayar cewa ba shugaba mai girman Annabi Muhammadu (SAW), mu kuma mu ce Annabi (SAW), shi ne mai girman duk wani mai girma da Allah ya taba yi. Duk wani babba tun da aka fara tarihi har ya zuwa zamanin Manzon Allah (SAW) har ya zuwa zamaninsa, wajen 1930 (wanda ya yi wannan littafi) ya ce Manzon Allah (SAW) shi ne mai girma mai daraja mai daukaka, madaukakin duk wani mai daukaka da aka taba yi.

Idan za a zauna a yi tarihin wani mai girma ko tarihin rayuwar wani mai girma to tarihi da haihuwar girman duk wani mai girma ya dace a yi, wanda shi ne manzon Allah (SAW). Wannan magana tana nan a cikin Alkur’ani don haka ta karbu. Manzon Allah (SAW) shi ne shugaban duk Annabawa, babu wanda ya kai Annabi girman girma. Amma game da batun kudubi kuwa, da za a tara hankalin halitta duka bai kai daya cikin goma na hankalin Kudubi ba, da za a tara ibadar halitta gabadaya bai kai daya cikin gama na ibadar Kudubi ba, da za a tara tsoron Allah duk halitta bai kai daya cikin goma na tsoron Allah Kudubi ba. Kudubi shi ne ran halittar, shi ne hadimin hadarar Allah a cikin halitta. An yi magana mai yawa a wannan bangare a cikin Jawahirul Ma’ani, ya kawo cewa yana da tsarki, yana da kaza; yana da kaza, wanda kyaftawar ido ba zai sauka ba daga kai ba sai an ga tsarin halittar Allah ya lallace.

Labarai Masu Nasaba

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)

Kudubi yana tare da kwayar zarrar kowace halittar Allah, shi yake isar mata da sakon magana, wanda bai zauna da wadannan mazaje ba sai ya ji magana ce mai girma, sai ya ga kamar an maida shi Allah, ya ce mai aka bar wa Allah ragowa, abun ba haka yake ba, abun mammaki da mai fadar wannan yana da wayewar da yake ganin fina-finai na Turawa, da ya ga wannan magana kai-tsaye a sarari.

Misali a kan Kudubi, Turawa suna da wani fim da suke shiryawa na Dirakula (Dracula) wani mai shan jini, abun kamar tatsuniya ce suke shiryawa, amma wani ya ce an yi fada ne da Daular Usmaniyya, wato daular Turkiya, akwai abubuwa da ya ba su tsoro sai suka maida wannan daular ta zamo daular da ke shan jini, amma ainihi wani sarki ne daga cikn daular Usmaniyya, amma ba haka abin yake ba, kila walitta yake nuna masu, kila wani abu ya nuna masu. Muhimmin abin da nake son in fada idan a wannan fim din wannan shu’umi (actor) ya sha jini ko ya ba wani jininsa (to wannan jini na Dirakula shi ne Kudubi), su da shi ke ba su san Allah ba, shi ya sa suka kawo misali da jinin jikin mutane, to duk wanda mutumin da ya sha sai ya rika jin duk wani motsi da halittar Allah, haka nan da sauro zai kada fukafukansa a karshen duniya da zai ji a kunnensa, wannan kenan.

Turawa suka shirya, kar ka ga ba su da addini, kwarewa ko sani cikin wadannan abubuwa. A’a suna da shi, suna da addini da malamai suna da Falsafofi, suna da Ruhubanai da kullum suke a cikin halwa. Idan kana bin irin wadannan fina-finai za ka ga abubuwan mamaki.

Akwai wani fim da kasar Ingila ta shirya na ‘The Seeker”, Falillahi, idan za ka kawo misali koda waye ka kawo muddin za a fahimci ilimi, Allah zai iya buga misali da sauro ko gizo-gizo, kafirai suka ce kuma misali ya kare da ake buga misali da sauro. Allah ba ya jin kunyar buga msali da komai, don haka nan mu ma za mu kawo don mu fahimci ilimi ba mu tsoron buga misali da The Seeker da Merlin da sauransu.

Yanzu wannan The Seeker din, idan ka lura yadda suka shirya fim din, shi Kudubi ne mai zaman kansa, amma shi kansa bai san kansa ba, shi kuma yana da wasu masu kiyayeshi, yana da wani kudubi Zaitu wanda shi ya san waye wannan, shi ya san sigar nan, kuma kiyaye shi yana hannun Zaitun nan, Allah ya hada shi da wasu mata, akwai wata ta iya tarbiyyantarwa, akwai wata Sufiya da duk wasu Kuduai ba su da tasiri a kanta, wannan abu duk akwai shi. Shehu Tijjanin Abul Abass (RTA), ya ce yafi mafatihul Kunuzi ta wani wajen su kuma sun fi shi ta wani wajen.

Sayyidina Kabiru ya za ci ya san duk Waliyyan Allah, sai da ya je Baitul Mukaddasi ya ga Abdulrazaki mutane sun kewaye shi yana ba da karatu, sai ya ga wani yaro a kwance yana bacci, sai ya zo ya yatshi yaro ya ce kai ba ka jin kunya duk mutane suna wajen Abdulrazaki suna karatu, sai ya ce ka kyale ni malam, ni wajen Razzaku nake karatu, mu ba a wajen bawan Razzaku muke ba, a wajen Razzaku muke karatu, sai ya ce yi kwanciyarka, sai ya ga cewa akwai aiki a gabansa.

To a cikin wannan fim din, akwai wata kalma da Zaitu yake fada wa wata mata da yake tafiya da ita, ya ce ki duba yau mu ne muradin Allah a kan kasa, Allah mu yake kallo a kan kasa, mu Allah ke nufi a kan kasa amma kuma ko gida ba mu da shi a doran kasa a daji muke yawo, wannan ya nuna cewa ba wai don kana waliyi shi kenan kai dan mai da nono ne, kai sai kaza da kaza ba.

Yayin da yake tafiya da wannan yaro, duk da ya dame su, sai ya ce ke wannan yaro da kike gani shi ne duniya gaba daya, wani ruhi ne, idan wannan yaro ya rushe shikenan duniya ta kare, duniya fanko ce, wannan yaro shi ne duniya.

Ilimin walitakka, ba wani ilimi ne sabo da aka kago ba , ilimi ne da dama yana nan tun farko, duk malamai masu hikima masu halwa suna nan da shi, akwai wani matsayi da Waliyi yake hawa, ya na samu ne daga zikiri da halwa da tunani da abin da Allah ya rubuta masu suke kaiwa wannan matsayi, suna jin halittar Allah kaf da kunnensu kuma wannan ba ta kare masu jin wancan ba, ba ta shagaltar da shi wancan ba, kuma yana harkokinsa na rayuwa yana baccinsa yana aurensa, kaga wannan ya fi karfin hankali, wannan Kudubi ke da irin wannan.

Sayyadi Ali, Allah ya kara masa yarda, shi ke maganar walitta, shi ne asalin Sufaye gaba daya, sunansa waliyi waliyen muminai wata rana yana kan hanyarsa ta zuwa yakI sai ya zo shigewa ta wajen da Annabi Sulaiman ya shige watau wadil Namli, daji ne na tururuwai, Salmanul Farisi ya kalli dajin bakikirin sai tururuwai, sai ya ce tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya halicci wadannan tururuwai kuma ya san adadinsu, sai Sayyadi Ali ya ce, zo in koya ma tasbihi baka iya tasbihi ba, ka ce tsarki ya tabbata ga Allah da Ya halicci wadannan tururuwai, amma wasu bayin Allah sun san adadinsu, ka gan ni nan, na san adadinsu, na san mata a cikinsu na san kuma san maza, haka nan kuma na san masu kwai na san marasa kwai.

Shehu Tijjani Abul Abassi, ya ce idan har Kudubi ya zama haka wanda shi kuma tsakaninsa da Annabi kamar yadda tururuwa take da tafiyar shaho a sama, shi Annabi shi shi ne kamar mai tafiyar shaho a sama (wato saurin tafiyar), shi kuma Kudubi shi yake daidai da tafiyar tururuwa a kasa (wajen yanayin sauri) haka nan ganinsa da na Annabi duk da wannan tsarki na Kudubi, to mun gode wa Allah, Manzon Allah (SAW) shi ne Annabin annabawa, malamin malamai.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa in sha Allah.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Annabi
ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yan Nijeriya Na Karbar Sakamakonsu Da Hannun Hagu A Wajen Tinubu – Atiku

Next Post

NDLEA Ta Kama Kilo 588 Na Miyagun Ƙwayoyi, Ta Ƙona Hekta 6 Na Gonakin Wiwi A Adamawa

Related

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)
Dausayin Musulunci

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

1 week ago
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)

4 weeks ago
Kyawawan Abubuwa Da Allah Ya Yi Wa Manzon Allah (SAW) Na Girmamawa
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah

1 month ago
Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan (7)
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan (7)

1 month ago
Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan (6)
Dausayin Musulunci

Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan (6)

2 months ago
Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)
Dausayin Musulunci

Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)

2 months ago
Next Post
NDLEA Ta Kama Kilo 588 Na Miyagun Ƙwayoyi, Ta Ƙona Hekta 6 Na Gonakin Wiwi A Adamawa

NDLEA Ta Kama Kilo 588 Na Miyagun Ƙwayoyi, Ta Ƙona Hekta 6 Na Gonakin Wiwi A Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Goron Sallah

GORON JUMA’A

October 3, 2025
NDLEA Ta Kama Kilo 588 Na Miyagun Ƙwayoyi, Ta Ƙona Hekta 6 Na Gonakin Wiwi A Adamawa

NDLEA Ta Kama Kilo 588 Na Miyagun Ƙwayoyi, Ta Ƙona Hekta 6 Na Gonakin Wiwi A Adamawa

October 3, 2025
Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

October 3, 2025
Tinubu Ya Gaza Wajen Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya — Atiku

‘Yan Nijeriya Na Karbar Sakamakonsu Da Hannun Hagu A Wajen Tinubu – Atiku

October 3, 2025
Raya Al’ada: Bikin Kalankuwa Na 2025 A Kano

Raya Al’ada: Bikin Kalankuwa Na 2025 A Kano

October 3, 2025
Za mu Inganta Fannin Karatun Alkur’ani – Gwamnan Jigawa

Za mu Inganta Fannin Karatun Alkur’ani – Gwamnan Jigawa

October 3, 2025
Yadda Sanata Barau Ke Samar da Masana Don Ci Gaban Kano

Yadda Sanata Barau Ke Samar da Masana Don Ci Gaban Kano

October 3, 2025
Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama

Bayan Shekara 20 Nijeriya Ta Sake Dawo Da Tsarin Bayar Da Hayar Kananan Jiragen Sama

October 3, 2025
Ƴansanda Sun Fara Aiwatar Da Dokar Sanya Baƙin Gilashi Mota A Legas

Ƴansanda Sun Fara Aiwatar Da Dokar Sanya Baƙin Gilashi Mota A Legas

October 3, 2025
Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho

Tashoshin Jiragen Ruwa Sun Samar Da Kashi 19.6 Na Fitar Da Kayan Da Ba Su Shafi Mai Ba—Dantsoho

October 3, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.