ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kadan Daga Hakuri Da Yafiya Da Rangwamen Annabi (SAW)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani and Sulaiman
1 year ago
Manzon Allah

Masu karatu, assalamu alaikum. Idan ba a manta ba, a makon jiya mun dauko darasi a kan kyawawan dabi’u da hasken sanin Allah da ake haihuwar annabawa da su.

Kamar yadda muka diga aya a makon na jiya, yanzu za mu ci gaba kadan kafin mu kammala mu koma darasinmu na yau. Duk wadannan Ilimai na Annabi (SAW) babu wani Malami da ya koya wa Annabi su ko kuma suka yi bita tare, kai bari ma, Annabi (SAW) ba’uwa ne (bai iya rubuta ko karatu ba) har Allah ya ba shi Annabta ya bayyana lamarinsa sannan ya sanar da shi kuma ya karantar da shi. Duk wanda ya binciki tarihin Annabi (SAW) zai tabbatar da hakan.

  • Gwamnati Ta Sake Haɗa Tubabbun Mayaƙan Boko Haram 5,000 Da Iyalansu
  • Gwamnonin Tafkin Chadi Sun Yi Taro Karo Na 5 Don Magance Matsalar Yankin

Allah Ubangiji ya tabbatar da hakan da fadinsa “wa allamaka malam takun ta’alam, wa kana fadlullahi alaika azima” Allah Ubangiji ya sanar da kai abin da ka kasance ba ka san shi ba, lalllai falalar Ubangiji a gare ka tana da girma. Annabi (SAW), shi ma ba shi da rowa, abin da Allah ya sanar da shi mu ma sai ya sanar da mu, “wayu allimukum malam takunu ta’alamun,” ma’ana yana sanar da ku abin da kuka kasance ba ku sani ba.

ADVERTISEMENT

Hankali ba ta iya kididdige baiwar Allah a kan Annabinsa, Baki ya gaza wurin yin bayanin baiwar Allah a kan Annabinsa ta yadda za a iya ganewa.

Alhamdulillah… yanzun za mu juya akalar karatunmu don jin wasu kadan daga cikin halayen Hakuri da yafiya da rangwamen Annabi (SAW). Lallai hakuri da juriya ma’ana dauke bala’i ka nuna kamar abin bai dame ka ba da hakuri a kan abin da mutum yake so ba ma’anarsu daya ba.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

Shi hakuri, ana nufin halin nutsuwa, in wani abu ya tayar maka da hankali amma a ga mutum cikin nutsuwa da kuma tabbata a kan nutsuwa lokacin da wasu abubuwa da ba makawa in aka yi wa mutum sai sun hargitsa shi amma ya dake a gan shi cikin nutsuwa bai yi fushi ba.

Ita kuma juriya cikin dauke bala’o’i, ita ce tsare rai cikin rashin damuwa lokacin da ake cikin tsananin damuwa, mutum ya nuna kamar abu bai faru ba.

Ita kuma yafiya ko rangwame, ita ce barin ramuwa ga wanda ya yi maka ba daidai ba.

Dukkan wadannan halaye, suna daga cikin wadanda Ubangiji ya ladabtar da ma’aikinsa (SAW) da su. Ubangiji yana fada masa a cikin hakkinsa “kuzil afwa, wa’amur bil ma’rufi, wa a’arid anil jahilin” ya rasulallahi ka yi rangwame, ka yi umurni da abin da shari’a ta saukar maka sannan kuma ka kauda kai ga jahilai masu yi maka wauta. An ruwaito daga Annabi (SAW) yayin da aka saukar masa da wannan ayar, ya ce ya Jibrilu mece ce fassarar wannan ayar, sai Jibrilu ya ce ni ma sai na tambayi masani (Allah), sai Jibrilu ya tafi tambaya (inda yake ganawa da Ubangiji) bayan ya dawo sai ya ce ya rasulallahi, “Ubangijinka yana horon ka da ka sadar da zumunci ga wanda ya yanke maka, ka ba wa wanda ya hana ka, ka yi rangwame ga wanda ya zalunce ka” wadannan su ne manyan dabi’u duk da cewa, akwai wasu hadisai da suke bayyana cewa, mutum ya yi zamansa a wuri daya ya fi, hadisin yana cewa “Gidanka ya isar maka (in ka san wanda ya yanke maka, zuwanka gare shi zai saukar da wutar bala’in da ke zuciyarshi, wannan zuwan ya fi zama a gida, amma in zuwanka wurinshi bala’in ne zai karu, zamanka ya fi zuwa) wanda ya hana ka, ka ba shi – in wani bala’in ba zai kara kunno kai ba, ka yafe wa wanda ya zalunce ka.”

Ubangiji ya kara cewa Annabinsa (SAW) “wasbir ala ma’asabak, inna zalika min azmil umur,” ma’ana ka yi hakuri kan abin da ya same ka, lallai hakuri kan bala’i yana daga cikin manyan abubuwa. “fasbir kama sabara ulul azmi minarrusul…” ka yi hakuri kamar yadda manya daga cikin Annabawa suka yi “wal ya’afu wal yasfahu…” ku yi afwa ku yi rangwame “ala tuhibbun an yagfirallahu lakum wallahu gafurun Rahim” shin ba ku son ku ma Allah ya yi muku gafara ne, Allah mai gafara ne kuma mai jin kai.

Imam Turmizi ya ruwaito hadisi daga Urwatu shi kuma daga uwar Muminai Sayyada A’isha ta ce, ba a taba kawo wa Annabi (SAW) zabin abu biyu ba face sai ya zabi mafi sauki, matukar mafi saukin bai zama zunubi ba, Annabi (SAW) bai taba fushi ba don wani ya taba shi sai dai in wani aka taba ko kuma akwai hakkin Allah a ciki. “Duk wanda ya jibinci lamarin Allah, shi ma Allah zai jibinci lamarinshi”

An ruwaito cewa yayin da aka karya hakorin Manzon Allah (SAW) a ranar yakin Uhudu, hakorin ya yi tsanani a gareshi, sai sahabbai suka ce “Ya rasulallahi, da ka yi musu bakar Addu’a” Sai ya ce musu, ba a aiko ni in tsine wa mutane ba sai dai in zama Rahma a gare su. Allah Ka shiryar da Mutanena, ba su sanni ba ne.

An ruwaito daga Sayyadina Umar RA ya ce: Na ba da fansar Iyayena a gare ka, Annabi Nuhu ya yi wa Mutanensa bakar addu’a da cewa “Allah kar ka bar ko digon kafiri daya a kan kasa, duk ka hallakar da su”. Ya Rasulallahi da ka yi irin wannan adu’ar a kanmu kafin Musulunta, da tuni mun halaka dukkanmu, an cutar da kai, an zubar maka da jini, an karya hakorinka amma duk da haka sai ka fadi alkhairi a kanmu ba ka yi mana muguwar addu’a ba. Amma rahama da tausayi da rangwame na Annabi (SAW), bayan ya yafe musu kuma sannan ya nema musu afuwa da kafa musu hanzarin cewa “Ya Ubangiji ba su sanni ba ne.”

Yayin da wani ya jefi Manzon Allah (SAW) da cewa, ya rasulallahi “ka yi adalci” a yakin Hunaini sai (SAW) ya ce “kaiconka! wa ye zai yi adalci in ban yi adalci ba, ashe na tabe” ya hana wanda ya yi nufin ya sare masa kai na daga Sahabbansa da fadinsa ya za kai da zuriyar da zai bari bayansa.

Wannan mutumi shi ne ake kira Zulkhuwaisarah, Mutum ne mai yawan Sallah da karatun Alkur’ani, sabida yawan Azumi duk idanuwansa sun faffada amma babu girman Annabi (SAW) a zuciyarsa. A ranar yakin Sayyadina Ali da tawagar khawarijawa aka kashe shi, Sayyadina Ali ya ce Annabi (SAW) ya fada masa a wannan yakin za a kashe shi, Sayyadina Ali ya ce a binciko gawarshi sabida Annabi (SAW) ba ya karya, an shafe tsawon lokaci ana neman gawarshi amma ba a gani ba, bayan duba gawarwakin da suka fada cikin wani Rami, sai gashi an zakulo gawarshi. Annabi (SAW) ya yi gaskiya.

Akwai wani Kafiri da ake kira Gaurasu bin Harisu, ya taba bijiro wa Annabi (SAW) da nufin kashe shi yayin da Annabi (SAW) shi kuma ya koma gefe daya jikin wata bishiya yana hutawa ya rataye takobinsa jikin bishiyar, sai Gaurasu ya lallabo ya dauki takobin ya ce wa Annabi (SAW) “Yau waye zai kare ka” take Annabi (SAW) Ya ce masa ‘Allah’ kawai sai takobin ta fadi, Annabi (SAW) ya dauki takobinshi ya ce wa Kafiri Gaurasu, “kai kuma waye zai kare ka yau?” sai ya ba da amsa cewa, ka zama fiyayyen wanda ya dauki takobi ko kuma abin da ka fada ya kare ka, ni ma shi zai kare ni, in ji Gaurasu. Sai manzon Allah (SAW) ya yafe masa, ya koma wurin mutanensa ya ce musu, na zo wurinku daga wurin mafificin mutane.

Yana daga cikin labarun Annabi (SAW) kan yafiya, yafewarsa ga Bayahudiyar nan da ta sa masa Guba cikin naman akuya, da aka kama ta ta ce, tana sane ta sa gubar da nufin cewa; In Annabi (SAW) sarki ne kawai, ya mutu a huta, in kuma da gaske Annabin Allah ne, Ubangijinsa zai kiyaye shi. A wata ruwaya, Annabi Ya sa a kashe ta sabida akwai wani sahabi da ya ci kuma ya rasu nan take. Ingatattar ruwaya ita ce, Annabi (SAW) ya yafe mata amma sabida mutuwar wani daga cikin Sahabbansa bayan cin gubar, Annabi (SAW) ya sa a kashe ta.

SAW
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ posts Bio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
SAW
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
  • Sulaiman
    Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026
  • Sulaiman
    An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”
  • Sulaiman
    Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

MASU ALAKA

Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

July 3, 2026
Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

June 26, 2026
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Jama’a Kan Ajiye Abubuwa Masu Fashewa Don Haƙar Ma’adanai Ba Bisa ƙa’ida Ba

Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Jama’a Kan Ajiye Abubuwa Masu Fashewa Don Haƙar Ma’adanai Ba Bisa ƙa’ida Ba

LABARAI MASU NASABA

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.