Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta duba albashin jami’an ƴansanda masu aiki yanzuda kuma ceto waɗanda suka yi ritaya daga halin matsananciyar yunwa da tsadar rayuwa.
Atiku ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Lahadi, 18 ga Oktoba, 2026, ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu.
Sanarwar ta koka kan yadda tsofaffin jami’an suka tsinci kansu a ƙuncin rayuwa, inda wasu ke karɓar Naira 29,000 kacal a matsayin fanshon wata-wata, yayin da wasu ke neman aikin share-share da goge-goge don ciyar da iyalansu. Atiku ya soki yadda gwamnatin Tinubu ta amince da ƙarin albashi ga dakarun soji amma ta yi watsi da na ƴansanda da ke fuskantar tsadar rayuwa su ma a kullum.
Haka kuma, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya zargi Shugaba Tinubu da kin sanya hannu kan Kudurin Dokar Ficewar Ƴansanda daga Tsarin Fansho (Police Exit Bill) da majalisa ta aika masa tun a watan Maris na 2026. Ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta ɗauki matakan da kundin tsarin mulki ya tanadar domin zartar da dokar ba tare da ɓata lokaci ba.
A ƙarshe, Atiku ya baje kolin shirinsa mai taken “Police Dignity Guarantee Plan” idan ya lashe zaɓen 2027, wanda ya haɗa da biyan dukkan basussukan fansho da garatuti, da kafa ƙa’idar mafi ƙarancin fansho mai tafiya da hauhawar farashin kaya, gami da samar da inshorar lafiya kyauta ga dukkan jami’an ƴansanda masu aiki da wanda suka yi ritaya.














