Wani mai magana da yawun ofishin jakadancin kasar Sin dake Japan, ya yi matukar Allah wadai da matakan baya bayan nan na mahukuntan Japan game haikalin Yasukuni, bayan da wasu jagororin kasar suka aike da hadaya zuwa haikalin, kana wasu daga membobin majalisar ministoci da yan majalisar kasar suka ziyarci wurin.
Jamiin wanda ya yi tir da matakin a jiya Asabar, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan batun, ya ce kasar Japan ta kaddamar da hare-haren danniya kan wasu kasashe da yankuna yayin yakin duniya na biyu, ta kuma aikata muggan laifukan yaki.
Ya ce haikalin Yasukuni, wuri ne da aka binne ajin farko na muggan jamian Japan da suka aikata laifukan yaki, wanda kuma ake amfani da shi yanzu haka a matsayin wani ruhi mai tasiri, kuma alamar farfado da karfin sojin kasar ta Japan.
Daga nan sai jamiin ya ce duk yadda jamian gwamnatin Japan suka yi kokarin boye dalilin ziyartar wannan haikali, ba za su iya boye hakikanin manufarsu, ta wanke laifukan mayakan kasar da suka aikata taasa ba, da yunkurin rufe laifukan da aka aikata a lokacin yaki, da sauya shaidu na tarihi, da share fagen gaggauta sake farfado da karfin sojin kasar ta Japan. (Saminu Alhassan)














