Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta
Mai taimaka wa babban sakataren MDD Guy Ryder wanda ya zo kasar Sin don halartar dandalin tattauna batun jagorancin duniya na Xiongan na shekarar 2026, ya bayyana wa ‘yan jarida a jiya 24 ga wannan wata, a sabon yankin Xiongan dake lardin Hebei na kasar Sin cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen daidaita tafiyar da harkokin duniya, kuma shawarwari hudu da kasar Sin ta gabatar sun dace da burin MDD. A cewarsa, hangen nesa da kasar Sin ta yi ya burge sassan duniya, kuma wannan ne kasa da kasa suke bukata a halin yanzu. Ryder ya bayyana cewa, MDD tana ci gaba da daukar kasar Sin a matsayin muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa. Ya ce, shawarwari na duniya guda hudu da kasar Sin ta gabatar suna shafar fannonin samun ci gaba, da kiyaye tsaro, da raya al’adu, da daidaita harkokin kasa da kasa da sauransu, wadanda suka dace da burin tsarin bangarori daban daban ciki har da burin MDD. A lokuta da dama, kasar Sin ta nuna goyon baya ga ra’ayin bangarori daban daban da kuma MDD, ta ce za ta tabbatar da kiyaye tsarin duniya a karkashin tushen MDD, da kuma odar kasa da kasa bisa tushen dokokin kasa da kasa. Ryder ya kara da cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da sauran kasashe masu tasowa na duniya ya kasance alamarta yayin da take daidaita tafiyar da harkokin duniya. Ya ce, a shekaru 81 da suka gabata, MDD na da membobi guda 51 ne kawai yayin da aka kafa ta, amma ya zuwa yanzu, yawansu ya karu zuwa 193, inda hakan ya nuna cewa, kasashe masu tasowa na duniya sun riga sun shiga harkokin duniya a dukkan fannoni. Amma kuma tsarin jagorancin harkokin duniya na yanzu bai mika cikakken ikon yin magana ga kasashe masu tasowa ba. (Zainab Zhang)



















