Li Qiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Nuna Kwarewar Sana’o’i Na Duniya Na Shekarar 2026
An bude gasar nuna kwarewar aiki karo na 48 a birnin Shanghai a jiya Talata, inda mutane 1,385 daga kasashe 68 za su fafata a fannoni 64 na gasar. Kasar Sin, na da wakilai 71 da za su fafata a fannoni 64 da aka tsara, wanda a cewar masu shirya gasar, ya hade sassa 6 da suka kunshi sufuri da jigilar kayayyaki, fasahar gine-gine, fasahar kere-kere da injiniyanci, fasahar sadarwa da yada labarai, kirkire-kirkire, da ayyukan zamantakewa da hidimomin kai. Gasar ta bana an yi mata take da ”kware a aikinka domin canza rayuwarka”, inda ta hada kwararrun matasa daga kowanne lungu da sako na duniya, domin su nuna gogewarsu da kuma musayar kwarewa a tsakaninsu. Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci bikin bude gasar tare da gabatar da jawabi. Li Qiang, ya ce shugaban kasar Sin Xi Jinping a cikin wasikar taya murna da ya aike ga taron kwarewar sana’o’i na duniya karo na 48, ya yaba da rawar da gasar ke takawa a matsayin dandalin musayar kwarewar sana’o’i ta duniya, kuma ya bayyana matsayin Sin na goyon bayan ci gaban harkokin kwarewar sana’o’i na duniya. Wannan taron mai taken “kwarewar sana’o’i tana haskaka makoma”, wanda hakan ya dace da ci gaban zamani. Li ya kuma gabatar da jawabi yana mai cew,a da farko, nasarorin ci gaban Sin suna dogaro da gudummawa ta musamman daga fannin kwarewar sana’o’i. Na biyu, Sin ta ci gaba da kokarin bunkasa karfin kwarewar ma’aikata. Na uku, tana yin hadin gwiwa wajen kafa kyakkyawar makoma ta ci gaban kwarewar sana’o’i. Firaministan Malaysia Anwar Ibrahim, da shugaban kungiyar kwarewar sana’o’i ta duniya Francis Hourant da sauran baki sun halarci bikin, kuma a cikin jawabansu, sun jinjinawa yadda gwamnatin Sin ta jima tana aiki tukuru wajen horar da kwararrun sana’o’i, wanda hakan ke ba da karfi ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewarta, kana yake ba da gudummawa mai muhimmanci a fannin habaka harkokin kwarewar sana’o'i na duniya da ci gaban matasa. Ci gaban kwarewar sana’o’i ya zama abin da gwamnatocin kasashe suka sa a gaba, kuma bangarori daban-daban na fatan karfafa gogewa tare da Sin, domin mayar da kwarewar ta zama wata muhimmiyar hanya ta hadin gwiwa dake kawo moriya ga kowa. (Mai Fassara: Suleiman Suleiman, Amina Xu)



















