Kakakin Ma’aikatar Cinikayya Ta Kasar Sin Ya Amsa Tambaya Dangane Da Matsayar Da Aka Cimma Tsakanin Sin Da Kungiyar EU A Kan Ababen Hawa
Kakakin Ma’aikatar Cinikayya Ta Kasar Sin Ya Amsa Tambaya Dangane Da Matsayar Da Aka Cimma Tsakanin Sin Da Kungiyar EU A Kan Ababen Hawa A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ya amsa tambayoyi daga ‘yan jarida, dangane da matsayar da aka cimma tsakanin Sin da kungiyar tarayyar Turai ta EU, game da batun ababen hawa masu aiki da lantarki da masu aiki da lantarki da kuma fetur. A cewar jami’in, Sin da EU sun shafe tsawon lokaci suna tattaunawa karkashin tsarin tuntuba game da cinikayya da zuba jari, sun kuma cimma wasu jerin matsaya, wadanda za su kyautata wanzar da daidaito da saita alakokin cinikayya tsakaninsu. Kazalika, karkashin ka’idojin martaba juna da tuntuba bisa daidaito, sassan biyu sun gudanar da shawarwari sosai, dangane da cinikayyar ababen hawa masu aiki da lantarki da masu aiki da lantarki da kuma man fetur, sun daidaita jerin sabanin cinikayya da abubuwan da suke mayar da hankali a kansu, kana sun kauracewa sake ta’azzarar sa-in-sar cinikayya, wanda hakan ya samar da yanayi bisa daidaito, wanda za a iya hasashen makomarsa kuma mai dorewa, a fannin raya cinikayya da zuba jari domin moriyarsu, irin yanayin da zai kyautata daidaito, da saita tare da inganta ci gaban alakar tattalin arziki da cinikayyarsu. (Saminu Alhassan)



















