Babban Bankin Kasar Sin Ya Bayyana Matsayinsa Kan Manufar Musanyar Kudin Kasar
Babban bankin kasar Sin ya bayyana matsayinsa kan manufar musanyar kudin kasar wato RMB jiya Alhamis 8 ga watan nan. Takardar bayani da ya fitar ta yi nuni da cewa, kasar Sin na aiwatar da manufar musanyar kudi bisa tushen la’akari da bukatun kasuwa kuma ta hanyar da ta dace, ta yadda kasuwa za ta taka muhimmiyar rawa wajen kayyade darajar musanyar kudin kasar. Babban bankin kasar ba zai kayyade darajar musanyar kudi ba, kana ba zai yi shisshigi cikin makomar darajar musanyar kudin ba na dogon lokaci, maimakon haka, aikinsa shi ne a kiyaye darajar musanyar kudin yadda ya kamata. Har wa yau, takardar bayanin ta ce, kasar Sin za ta aiwatar da tsare-tsaren shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, da kawo sauye-sauyen salon bunkasa tattalin arziki, da habaka bukatun cikin gida, da fadada bude kofa ga kasashen waje, da zurfafa hadin-gwiwa tare da sassan kasa da kasa a harkokin kudade, da kara shiga cikin aikin inganta tsarin shugabancin duniya ta fuskar kudade, a wani kokari na tabbatar da kwanciyar hankalin tattalin arziki da kudi a duk fadin duniya. (Murtala Zhang)



















