Matakin Sin Na Gabatar Da Sunan ‘Yar Takarar Mukamin Babban Daraktan WHO Ya Shaida Matukar Goyon Bayanta Ga Tsarin Cudanyar Sassa Da Dama
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce gabatar da sunan Dr. Song Li da kasar Sin ta yi, a matsayin ‘yar takarar mukamin babban daraktan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, ya shaida matukar goyon bayan kasar ga tsarin cudanyar mabambantan sassa da ita kanta hukumar ta WHO. Mao Ning, ta bayyana hakan ne a Alhamis din nan, yayin taron manema labarai da ya gudana, lokacin da take amsa tambaya mai nasaba da hakan, inda ta ce a gabar da tsarin cudanyar mabambantan sassa ke fuskantar tarin kalubale, kuma ake bukatar gudanar da matakai masu yawa a fannin ingiza nagartar kiwon lafiya a duniya, rawar da babban daraktan WHO zai taka, musamman a bangaren sarrafa akalar hukumar, karkashin sabbin sauye-sauye da yanayi daban daban, za ta haifar da daidaito da ci gaba mai dorewa. Jami’ar ta ce yadda Sin ta gabatar da sunan Dr. Song, ya shaida aniyarta ta yin aiki tare da dukkanin sassa wajen hada karfi, don ingiza gina al’ummar duniya mai ingantaccen tsarin kiwon lafiya na bai daya, kana ya nuna matukar goyon bayan Sin ga tsarin cudanyar mabambantan sassa da ita kanta hukumar ta WHO. (Saminu Alhassan)



















