CMG Da Gwamnatin Lardin Jiangsu Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar “Shirin Karfafa Manyan Kamfanoni”
A yau Talata a birnin Nanjing, an gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar “shirin karfafa manyan kamfanoni” tsakanin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG da gwamnatin lardin Jiangsu, kana an gabatar da jerin ayyukan yada labarai na hadin gwiwa. Shen Haixiong, shugaban CMG ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. A jawabinsa Mr. Shen ya ce, a matsayin babban rukuni mafi girma, kuma mafi nau’ikan ayyuka da yada labarai ga wurare mafi yawa a duniya a yau, “shirin karfafa manyan kamfanoni” na CMG na ci gaba da karfafa wa manyan kamfanonin Sin gwiwa don su zama sahun gaba da fadada tasirinsu a duniya. Ya ce CMG zai ci gaba da yada labaran da suka shafi Jiangsu, da kara hadin gwiwa wajen karfafa wa manyan kamfanonin gwiwa, da zurfafa hadin gwiwar kirkire-kirkire tsakanin gwamnatin tsakiya da mabambantan wurare na kasar, kana da amfani da hanyoyin kirkire-kirkire wajen taimaka wa manyan kamfanonin Jiangsu yada tasirinsu ba iyaka. Haka zalika a yau din, an gudanar da taron “fafatawar fasaha: babban baje kolin fasahar amfani da na’urorin mutum-mutumin inji, karo na farko” na CMG, zangon Nanjing. (Amina Xu)



















