Duk da taazzarar kika-kakar cinikayya, da karan-tsaye da tsarin hada-hadar hajoji na duniya ya fuskanta, an bude dandalin shekara-shekara na tattauna manufofin hada-hadar kudi na 2026 a kan lokaci.
Wani binciken jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ya nuna yadda kaso 82.98 bisa dari na masu bayyana mahangarsu ta intanet, suka gamsu cewa ci gaba da kiran wannan taro da kasar Sin ke karbar bakunci, ya nuna kudurinta, da karfin gwiwar zurfafa sauye-sauye a fannin hada-hadar kudi da kara bude kofa da karfafa musaya a fannin hada-hadar kudi tsakanin kasa da kasa, da ma hadin gwiwar sassa daban daban. Kazalika, hakan ya shaida kwazon kasar Sin na kokarin magance manyan kalubalen dake fuskantar tsarin jagorancin tattalin arzikin duniya, wato batun yadda za a iya daidai harkar tsaro da ingancin ayyuka.
Yayin binciken, kaso 81.43 bisa dari na masu bayyana raayoyi sun amince, cewa karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a fannin hada-hadar kudi da Sin ke yi, ya taimaka wajen fadada samar da kafofin gudanar da hada-hadar kudi ga kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasa, kana ya samar da babban tallafi ga ci gaban tattalin arzikinsu. Har ila yau, kaso 84.49 bisa dari na ganin ci gaban kasar Sin a fannin bude kofofin hada-hadar kudi, da kwazonta wajen ingiza hadin gwiwar kasa da kasa a fannin, ya taimaka wajen karfafa kwarin gwiwa, da agazawa daidaiton kasuwannin hada-hadar kudi na duniya. (Saminu Alhassan)














