Wang Yi Ya Halarci Taron CICA Karo Na Bakwai
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, wanda ya kasance wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, a taron karawa juna sani karo na bakwai, dangane da zakulo dabarun gina cudanya da kwarin gwiwa a shiyyar Asiya ko CICA a takaice, ya gabatar da jawabi a taron na jiya Alhamis, inda ya ce, kasashen Asiya ne suka kafa dandalin CICA, da nufin gudanar da shawarwari da hadin gwiwa. Kuma tun kafuwarsa, CICA ya taka rawar gani wajen samar da nasarar muhimman kudurinsa biyar, wato wanzar da zaman lafiya tare, da bunkasa hadin gwiwa mai cikakken tsari bisa matakan gina kwarin gwiwa, da nacewa manufar cudanyar mabambantan sassa, da aiki tukuru wajen karfafa tushen gaskiya don cimma zaman lafiya da tsaro a Asiya. Ya ce, kasar Sin na matukar jinjinawa kwazon kasar Azerbaijan, dangane da bunkasa hadin gwiwar dandalin yayin kasar ke jagorancinsa, kuma Sin a shirye take ta ci gaba da nuna matukar goyon baya da shiga a dama da ita a ayyukan dandalin. Wang ya kara da cewa, a gabar da ake ta fuskantar sauye-sauye cikin sauri irin wadanda ba a ga irinsu ba a cikin wani karni, ta hanyar hade kan alummu wuri guda bisa makomar bai daya, da kasancewa a bangaren gaskiya a tarihi, da rungumar goyon bayan juna, da hadin gwiwa ne kadai kasashen Asiya za su wuce gaba a lokuta daban daban, kana za su iya sauya kalubale zuwa damarmaki da hada hannu wajen samar da makoma mai nagarta. (Saminu Alhassan)



















